Tsawa ta kashe ’yan kwallo biyu

Rahotanni daga kasar Jamaika sun ce a ranar Asabar da ta wuce tsawa ta hallaka wadansu matasa biyu a yayin da suke buga kwallo,  sannan rahoton ya ce tsawar ta jikkata wadansu matasa hudu.

Al’amarin ya faru ne lokacin da matasan suke buga gasar kwallon kafa ta makarantun sakandare da ke yankin a filin wasa na Kingston East da ke Kingston a Jamaika,

’Yan kwallon da tsawar ta hallaka  sun hada da dan kwallon Sakandaren Wolmer Boys School da kuma na Sakandaren Jamaica College.

Al’amarin ya faru ne a zango na biyu  a daidai lokacin da kulob din Wolmers ke kan gaba da ci 2-1.  Kwatsam ba zato, ba tsammani sai aka ji wata tsawa mai karfi inda nan take ’yan kwallo shida suka zube kasa warwas.  Kafin a kai su wani asibiti mafi kusa mutum biyu daga cikinsu rai ya yi halinsa yayin da sauran suka farfado bayan an yi musu magani.

Rahoton ya ce dan kwallon Wolmer Frances da dan kwallon JC, Terrence Francis da dan kwallon Wolmers  Dwayne Allen na daga cikin matasan da suka jikkata a yayin tsawar.

ADVERTISEMENT

Tuni mahukunta gasar suka mika sakon ta’aziyyarsu ga iyalan ’yan kwallon da suka rasu da kuma jajanta wa wadanda suka jikkata saboda tsawar.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya