Da Dumi Dumi

Tsige Trump: Kan sanatoci ya rabu

Ana samun rashin jituwa tsakanin ’yan Jam’iyyar Republican mai mulki a Amurka da na Jam’iyyar  Democrats a Majalisar Dattawan kasar sakamakon dokokin da aka gindaya yayin sauraron kudirin tsige Shugaba Trump na kasar.

’Yan Jam’iyyar Democrats dai na bukatar a bayar da dama domin kawo shaidu da takardu a lokacin da za a saurari karar, inda suka ce wannan ce hanyar da za a yi adalci kawai.

Daya daga cikin jiga-jigan ’ya’yan Jam’iyyar Democrats, Chuck Schumer ya ce sakon imel din da aka bankado a ’yan kwanakin nan, wanda aka tura wa kasar Ukraine ya sa dole a yi komai a bayyane.

Jagoran Jam’iyyar Republican a Majalisar Datawan Amurka, Mitch McConnell ya ce bai hana a kira shaidu ba, sai dai yana da shakku kan abin da shaidun za su fada.

A makon JIya ne dai Majalisar Wakilan Amurka ta tsige Shugaba Trump sakamakon samunsa da laifin yin karan-tsaye ga dimokuradiyya da kuma saba ka’idojin aiki.

ADVERTISEMENT

Shugaba Trump ne na uku a jerin shugabannin Amurka da aka taba tsigewa a tarihi.

Sai dai ana ganin da wuya ya sauka daga kujerarsa saboda jam’iyyarsa ta Republican ce ke da rinjaye a Majalisar Dattawan kuma a nan ne za a gudanar da muhawarar karshe kan batun tsige shi.

Ana zargin Trump da matsin lamba ga Shugaban Ukraine domin kaddamar da bincike kan abokin takararsa na Jam’iyyar Democrats wato Joe Biden.

Ana zargin cewa Mista Trump ya yi haka ne ta hanyar dakatar da taimakon soji ga kasar da kuma sharadin sai sun bayar da hadin kai zai ziyarci kasar. Ana sa ran fara muhawarar a watan Janairun badi, bayan hutun Kirsimati da sabuwar shekara, kamar yadda BBC ya ruwaito.

…Masu neman shugabancin Amurka sun goyi bayan tsige shi

’Yan takarar Shugaban Kasar Amurkar 7 da ke kan gaba a Jam’iyyar Democrats sun tafka muhawara a makon jiya, tare da caccakar Shugaba Donald Trump inda suka bayyana shi a matsayin Shugaba mafi gurbacewa a tarihin kasar.

Dukkan ’yan takarar da ke neman jam’iyyar ta tsayar da su domin fafatawa da Trump a zaben Shugaban Kasa a badi, sun ce suna goyon bayan matakin Majalisar Wakilai na amincewa da daftarori biyu na tsige Trump, saboda zarginsa da yin amfani da mukaminsa ba bisa ka’ida ba domin amfanin kansa a siyasance, da kuma kawo cikas ga zaman majalisa.

“Akwai bukatar mu dawo da martabar ofishin Shugaban Kasa,” inji tsohon Mataimakin Shugaban Amurka, Joe Baiden, wanda shi ne ke kan gaba a yiwuwar tsayar da shi takara a Jam’iyyar Democrats.

Sanata Bernie Sanders wanda shi ne na biyu a bayan Baiden a kuri’un ra’ayoyin jama’a, ya kira Trump “makaryaci” da ya sayar da al’ummar Amurka masu aiki.

’Yan takarar sun ci gaba da caccakar Trump, duk da yake a wasu lokuta sukan dawo caccakar junansu.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya