✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsofaffin gwamnonin da aka daure a gidan yari

A ranar Juma’ar da ta gabata ce tsohon Gwamnan Jihar Abiya Mista Orji Uzor Kalu ya shiga sahun tsofaffin gwamnonin da aka daure a gidan…

A ranar Juma’ar da ta gabata ce tsohon Gwamnan Jihar Abiya Mista Orji Uzor Kalu ya shiga sahun tsofaffin gwamnonin da aka daure a gidan yari sakamakon samunsu da almundahana lokacin da suke mulki. An yanke wa Kalu hukuncin daurin shekara 12, bayan da alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, Mai shari’a Mohammed Idris ya same shi da lshi da wadansu mutum biyu da almundahanar Naira biliyan 7.65.

Lamarin ya faru tun lokacin Mista Kalu yana Gwamnan Jihar Abiya inda ya zama Sanata a zaben da ya gabata.

Mista Kalu dan Jam’iyyar APC ce mai mulki da Shugaba Muhammadu Buhari ke cikinta.

Ba a cika samun kotu na yanke wa ’yan siyasa irin wannan hukuncin da aka yanke wa Mista Kalu ba a Najeriya, duk da cewa ba sabon abu ba ne, ya faru da wadansu tsofaffin gwamnoni.

Wadansu daga cikin tsofaffin gwamnonin da irin wannan hukuncin ya rutsa da su sun hada da:

Joshua Dariye: Tsohon Gwamnan Jihar Filato wanda a cikin watan Yunin bara aka yanke wa hukunci daurin shekara 14 sakamakon samunsa da laifin almundahanar Naira biliyan 1.6

Diepreye Alamieyeseigha (Marigayi): Tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa wanda a cikin watan Yulin 2007 aka yake masa hukuncin daurin shekara biyu a kan laifuffuka shida na almundahanar kudi da suka kai Naira biliyan 1.6

James Ibori: Tsohon Gwamnan Jihar Delta wanda a Afrilun 2012 aka yanke masa hukuncin daurin shekara 13 kan laifuffuka 10 da suka shafi kulla makirici domin almundahana da fitar da kudi ba kan ka’ida ba (Dala miliyan 77)

Jolly Nyame: Tsohon Gwamnan Jihar Taraba wanda aka yanke wa hukuncin shekara 28 kan laifuffuka daban-daban har 41.