✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon babban alkalin Kano Shehu Atiku ya rasu

Tsohon babban alkalan jihar Kano, mai shari’a Shehu Atiku ya rasu. Kakakin kotunan jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim wanda ya tabbatar da rasuwar a wata…

Tsohon babban alkalan jihar Kano, mai shari’a Shehu Atiku ya rasu.

Kakakin kotunan jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim wanda ya tabbatar da rasuwar a wata sanarwa ya ce marigayin ya rasu ne da yammacin ranar Lahadi bayan wata gajeruwar jinya.

Marigayi Shehu Atiku dai ya yi ritaya daga aikin gwamnati ne a shekara ta 2015, kuma za a rika tunawa da shi kan irin rawar da ya taka a shari’ar wasu bankuna da suka durkushe duk da yinkurin da suka yi na bashi toshiyar baki.

Kazalika, an ce ya ki bayar da kai bori ya hau kan irin barzanar da aka sha yi wa rayuwarsa kan irin hukunce-hukuncen da ya yanke lokacin da ya ke kan aiki.

Tuni dai aka yi jana’izarsa a Kano kamar yadda adiinin Musulunci ya tanada.