✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon dan kwallon Arsenal Robert Pires ya ziyarci Legas

A ranar 22 ga watan Satumbar 2013 ne, shahararren tsohon dan kwallon Arsenal da ke Ingila Robert Pires ya ziyarci Legas a matsayinsa na babban…

Robert Pires tare da wasu daga cikin magoya bayan kulob din Arsenal da ke LegasA ranar 22 ga watan Satumbar 2013 ne, shahararren tsohon dan kwallon Arsenal da ke Ingila Robert Pires ya ziyarci Legas a matsayinsa na babban bako a gasar kwallon matasan Afirka da kamfanin sadarwa na Airtel ya shirya tare da hadin gwiwar kulob din Arsenal da ke Landan  a birnin Legas. Pires ya halarci bikin rufe gasar ce a matsaytinsa na babban bako da kuma jakadan kulob din Arsenal.
Gasar wacce ta hada matasa maza da mata a wasanni daban-daban, a ranar ce aka yi bikin kawo karshenta inda manyan baki daga sassan duniya ciki har da Pires suka halarta.
Kamfanin sadarwa na Airtel  tare da hadin gwiwar kulob din Arsenal sun shirya gasar ce don zakulo matasan ’yan kwallo daga Nahiyar Afirka don amfanin kasa da sassan duniya.
kasar Tanzaniya ce ta kasance ta daya a bangaren mata a gasar bayan ta lallata ta Kenya da ci daya mai ban haushi.
A bangaren kwallon maza kuma, Zambiya ce ta lashe Nijar a bugun daga kai sai mai tsaron gida da ci 7-6 a wasan karshe bayan an tashi wasa da ci 1-1.
Jim kadan da tashi wasan ne sai babban bako Robert Pires ya raba kyaututtukan yabo ga wadanda suka samu nasara daga nan kuma ya yi jawabi a madadin kulob din Arsenal.
Bayan nan sai kamfanin na Airtel ya shirya liyafar cin abincin dare ga Pires inda aka gayyato wasu daga cikin masu yin hulda da kamfanin na Airtel da kuma magoya bayan kulob din Arsenal mazauna Legas zuwa wani dakin sayar da abinci (restuarant) da ke birnin Legas.
A wurin cin abincin ne aka ba jama’a damar yi wa dan kwallon tambayoyi musamman wadanda suka shafi kulob  din Arsenal inda Pires ya rika ba su amsa.  A washegari ne Pires ya ziyarci wata makarantar firamare mai suna Oremeji Primary School daya daga cikin firamare shida da kamfanin sadarwa na Airtel ya gina a matsayin gudunmawarsa don karatun ’ya’yan talaka a birnin Legas kafin ya zarce hedkwatar kamfanin na Airtel inda ya gana da shugabanni da ma’aikatan kamfaninj ciki har da shugaban kamfanin Segun Ogunsanya inda daga bisani aka zarce da shi Ofishin Jakadancin Birtaniya da ke birnin Legas kuma aka shirya masa liyafar cin abinci.
Kafin dan kwallon ya koma Ingila sai da ya ziyarci gidan Talabijin na Channels Tb News da wasu daga cikin tasoshin rediyo a birnin na Legas da suka hada da Nigeria Info da Cool FM da kuma Wazobia FM.
Tuni dan kwallon ya koma kasar haihuwarsa Ingila.