✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon dan kwallon Najeriya Philip Osondu ya rasu

Rahoton da kafar watsa labarai ta Naija news ta kalato ya ce tsohon dan kwallon Najeriya, Philip Osondu ya rasu.  Ya rasu ne a ranar…

Rahoton da kafar watsa labarai ta Naija news ta kalato ya ce tsohon dan kwallon Najeriya, Philip Osondu ya rasu.  Ya rasu ne a ranar Juma’ar da ta wuce a wani asibiti da ke Beljiyam.

Rahoton ya ce Osondu da kansa ya je asibiti a ranar Alhamis don a duba lafiyarsa inda rai ya yi halinsa washegari.

Dan shekara 48 Osondu ya yi wa Najeriya kwallo a matakin matasa musamman a kungiyar kwallon kafa ta U-16 amma bai taba yi wa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles kwallo ba.

Ya taba lashe dan kwallon da ya fi nuna kwazo a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya na ’yan kasa da shekara 16 da aka yi a Kanada a 1987 inda tsohuwar Tarayyar Sobiyet ta lallasa Najeriya a wasan karshe.

Ya taba yi wa kungiyar kwallon kafa ta Anderletch da ta RWDM dukkansu a Beljiyam kwallo daga nan ya yi ritaya.  Bayan ya yi ritaya sai ya samu aiki a Beljiyam kuma ya ci gaba da zama a can kafin rai ya yi ha,linsa a ranar Juma’ar da ta wuce.

An haifi Osondu ne a garin Aba a 1971.

a Anderletch da ta RWDM kwallo daga nan ya yi ritaya.  Bayan ya yi ritaya sai ya samu aiki a Beljiyam kuma ya ci gaba da zama a can kafin rai ya yi ha,linsa a ranar Juma’ar da ta wuce.

An haifi Osondu ne a garin Aba a shekarar 1971.