✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsumagiiyar kan hanya

Assalamu alaikum don Allah Aminiya ku ba ni dama in yi tsokaci a kan mummunar akidar nan ta SAK wadda ta samo asali sakamakon neman…

Assalamu alaikum don Allah Aminiya ku ba ni dama in yi tsokaci a kan mummunar akidar nan ta SAK wadda ta samo asali sakamakon neman kai da kuma gajiya da mutanen Najeriya suka yi da Jam’iyyar PDP har a wancan lokaci ake yi wa lakabi da ‘shegiyar uwa’ hakan ya sa aka dukufa da rokon Allah da haduwar jam’iyyun adawa da kuma  samun ingantaccen zabe wanda ya kawar da gwamnatin PDP da ba da damar kafa gwamnatin APC da mutanen Najeriya musamman Hausawa suka yi imani da samun kwarin gwiwar cewa wannan gwamnati ta APC za ta cire musu kitse a wuta amma kash! Sai ga shi a yau Jam’iyyar APC ta zamo mana karfen-kafa har ta fi waccan shegiyar uwar barna da lalata kasa. Ba na son tsanantawa, sakamakon abin da kowa ya ji ko ya gani ya faru a Kano ba jam’iyyar siyasa ba wadda ta yi babatu a kan mulkin PDP.

Hakazalika a karkashin wannan mummunar akidar  an zabi wadansu ’yan siyasa a 2015 amma ba su tsinana komai ba sai ga shi a zaben bana ma sun koma ga mukamansu sakamakon buya a karkashin SAK duk da cewa akwai dalilai da yawa da suke rura wutar annobar SAK kamar haka;

  1. Mulkin zalunci na PDP wanda a wancan lokacin ana neman kai da shi, ana son a samu sauyi a kasa sai ga shi ana samun ci gaban mai hakar rijiya.
  2. Rubabbun ’yan siyasa daga bangaren masu mulki wadanda suka kasa tabuka abin a zo a gani, haka su ma ’yan adawa ta hanyar kin bai wa ingantattun ’yan takara tikitin takara.
  3. Malaman addini, amma marasa jin tsoron Allah, suna fadin son zuciyarsu da sunan addini, masu fassara nassi ba yadda yake ba ko kuma ba a muhallisshahid ba wadanda kuma suka yawaita a wannan zamani.
  4. Jahilcin mutanenmu, mafi yawan mutane ba su san hakkokinsu a kan wadanda suke zaba ba, ba su san illar zabar baragurbin ’yan siyasa ba, ba su san irin karfin ikon da kuri’arsu take da ita ba wajen canja duk wani azzalumin shugaba kuma ko a wace jam’iyya ne ba.
  5. Rashin wayar da kan jama’a daga ’yan jarida da masu fashin baki da kuma kungiyoyi masu rajin karewa da kuma habbaka dimokuradiyya a kan illar zabar jam’iyya ba mutum ba.

Daga karshe nake cewa ya kamata ’yan Najeriya musamman Hausawa mu dawo daga daure wa karya gindi, mu dawo daga rakiyar jam’iyya, ya kamata mu dawo daga rakiyar barayin Dala da na Naira. Ya kamata mu daina goyon bayan masu barci da dumama kujera. Ya kamata mu nemi sauyi na hakika ta hanyar zabar mutanen kirki, mu dawo daga rakiyar maciya amana wadanda kujerar mulkinsu ta fi rayukan wadanda suke mulka.Ya kamata a bai wa mutanen kirki damar tsayawa takara kuma mu zabe su  a kowace jam’iyya ce.

Daga Kwamared Abdulmutallib Aliyu Tiga 08039520126.