Ranar Lahadin da ta gabata aka yi kasaitaccen bikin nadin Alhaji Tukur Wurno a matsayin Sarkin Hausawan Oshodi, wanda Sarkin Hausawan Jihar Legas, Alhaji Aminu Yaro Dogara ya yi bayan da jama’a suka amince da hakan.
Wani dattijo da ya yi jawabi a madadin sauran jama’a ya bayyana wa sarki Aminu cewa Alhaji Tukur ya dade yana dawainiya a kan duk wani abu da ya shafi Bahaushe da ma duk wani dan Arewa mazaunin unguwar ta Oshodi tun kafin a gabatar da sunansa.
Da yake jawabi jim kadan da nadin, Sarki Aminu ya ce ya amince da nada Alhaji Tukur ne saboda shi ne jama’ar suka ce suna so, kuma yana fata za su yi masa biyayya, wadda ta ita ce zai kara samun karfin gwiwar ci gaba da yi musu hidima, kamar ko ma fiye da yadda yake yi a da.
Ya bukaci sabon sarkin ya san cewa rashin adalci na iya jawo masa da-na-sani, “Domin kuwa duk shugaban da ba ya adalci, idan bai ga hukunci daga nan duniya ba, to ya sani cewa zai koma ga Allah, don haka ya nemi ya kasance mai adalci da hangen nesa wajen tafiyar da mulkinsa.
Shugaban kungiyar Yarabawa zalla (OPC ), Otunba Gani Adams, wanda ya halarci taron, ya tofa albarkacin bakinsa, inda ya yi fata za a ci gaba da samun hadin kai tsakanin sabon sarkin da jama’arsa. Dangane da dangantakar da ke tsakanin Hausawa da Yarabawa sai ya yi fata lamarin zai kara kyautatuwa da yake yanzu kowa ya kara ilmin fahimtar rayuwa wajen gane cewa. tashin hankali ba abin da yake samarwa sai koma-baya ga al’umma.
Ya yi kira ga al’ummomin biyu da ma sauran al’ummun Najeriya, a duk inda suka samu kansu, su zamo masu kaunar juna, domin ba wanda ya fi Allah sanin dalilin da ya sa Ya yo mu wuri guda.
Shi ma dan wasan kwaikwayo Chidi Mokeme cewa ya yi bikin ya kayatar da shi kuma haka ya kamata a ce ’yan Najeriya na zaune, suna kyautata dankon zumunta da ke tsakaninsu.
Emeka Ike, shi ma wani dan wasan kwaikwayo, cewa ya yi yana alfahari da yawan kabilun da Allah ya albarci Najeriya da su, sai dai fatansa shi ne a ci gaba da hankuri da zaman tare.
Shi kuma sabon sarki Alhaji Tukur fata ya yi Allah Ya ba shi ikon daukar nauyin da aka dora masa. Ya bukaci daukacin mutanen da suka halarci bikin su taya shi addu’a don ya kai ga cin nasara.
Tukur Wurno ya zama Sarkin Hausawan Oshodi
Ranar Lahadin da ta gabata aka yi kasaitaccen bikin nadin Alhaji Tukur Wurno a matsayin Sarkin Hausawan Oshodi, wanda Sarkin Hausawan Jihar Legas, Alhaji Aminu …