✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Turkiyya na fama da zanga-zanga

An shafe kwanaki ana turka-turkar zanga-zanga a kasar Turkiyya, al’amarin da ya zamar wa Firayiministan kasar Recep Tayyip Erdogan babban kalubale a mulkinsana tsawon shekara…

An shafe kwanaki ana turka-turkar zanga-zanga a kasar Turkiyya, al’amarin da ya zamar wa Firayiministan kasar Recep Tayyip Erdogan babban kalubale a mulkinsana tsawon shekara 10. ’yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa da ruwan zafi don tarwatsa masu zanga-zanga, amma duk da haka mutane suka yi biris, ind adaukacin biranen kasr, wadanda suka hada da Ankara babban birnin Turkiyya
Dubban Turkawa sun taru an dandalin Taksim, har tskwon kwana shida suna ta kwakwazon nuna adawa da Gwamnatin Erdogan, shi kuwa ya ce a yi watsi da masu zanga-zanga, don  “masu tsattsauran ra’ayi ne” da “’yan baranda.” Su kuwa suka mayar da masa da martani cewa:
“’Yan baranda sun bayyana! Ina Tayyip?” cincirindon mutane na ta yi masa ihu.
Mataimakin Firayiminista, Bulent Arinc ya roki gafarar masu tarzoma, musamman kan yadda ’yan sanda suka tsaurara wajen tunkarar masu zanga-zangar, al’amarin da kasar Amurka ta yi maraba da shi.
Wannan tarzoma da ta baibaye daukacin kasar, ta samo asali ne bayan da ’yan sanda suka jefa wa masu zanga-zanga barkonon tsohuwa, a lokacin da ka gudanar da zanga-zangar lumana, don nuna adawa da gina wurin shakatawa a birnin Istanbul.
 “Ina neman afuwar wadanda suka samu kansu a yamutsin tashin hankali, saboda kishinsu na kula da muhalli,” inji shi. Ya kuma kara da cewa wannan neman afuwar tasa ba ta hada da masu “tayar da tarzoma ba.”
Ya yi wannan jawabi ne a lokacin da Erdogan ya ficre daga kasar, zuwa kasar Afirka ta Arewa, ind aya yi biris da matsalar da yake fama da ita a cikin gida.
Mutum biyu suka rasa rayukansu a artabun da aka yi tsakanin jami’an ’yan sanda da masu zanga-zanga, kamar yadda jami’an kula da lafiya suka bayyana,. Kuma masu fafutikar hakkin dan Adam sun bayyana cewa an raunata dubban mutane. Ita kuwa gwamnati ta ce wadanda suka jikakta duk ba su wuce mutum 300 ba.
A farkon zanga-zangar, dandalin Taksim yua cika tamkar ana bukukuwa, inda Turkawa suka yi ta busa taba, suna rera wakoki ta cikin kakakin magana, inda ’yan kwallo suka kama hannayensu. Ana cikin haka sai ’yan sanda suka harba barkonon tsohuwa  da ruwan zafi.
Mafi yawan masu zanga-zangar na ta aikewa da sakonnin ta kafar sadarwar intanet, sun kuma koka kan yadd akafafen yada labarai ba sa yi wa duniya bayani kana halin da ake ciki.
kungiyar ’yan kwadagon kasar Turkiyya (KESK), wadda ’ya’yanta suka kai kimanin mutum dubu 240 tana goyon bayan wannan zanga-zanga, don haka ma ta kaddamar da yajin aiki na kwana biyu. Kamar yadda mai Magana da bakinsu, Baki Cinar ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.