Da Dumi Dumi

U-17:  Yau Eaglets za ta yi wasanta na uku da Australia

Kocin Golden Eaglets Manu Garba
Kocin Golden Eaglets Manu Garba

A ci gaba da fafatawa a Gasar Cin Kofin Duniya na ’Yan Kasa da Shekara 17 da  ke gudana a Brazil, a yau Kungiyar Golden Eaglets taNajeriya za ta yi wasanta na uku da takwararta ta Austireliya. Wasan zai gudana ne da misalin karfe 9 na dare agogon Najeriya.

An fara gasar ce a ranar Asabar da ta gabata, inda Najeriya ta yi wasanta na farko da kasar Hungary kuma aka tashi wasan Eaglets ta yi nasara da ci 4-2.  Sai a ranar Talatar da ta wuce Eaglets ta yi wasa na biyu da Ecuador, kuma ta samu nasara da ci 3-2.  Sai kuma yau da za ta yi wasa na uku da Austireliya.

Tuni Golden Eaglets ta haye zuwa zagaye na biyu, bayan ta hada maki 6 a wasanni biyu.  Ke nan ko ta samu rashin nasara a wasan yau, ta riga ta haye mataki na gaba.

Golden Eaglets wacce ke fafatawa a rukunin B ita ce ta farko a saman tebur da maki 6 sai Ecuardor ke biye da maki 3 sai Austireliya ta uku da maki 1 sai Hungary ta hudu ita ma da maki 1.

Idan za a tuna Najeriya ce ta fara lashe wannan kofi a 1985, kuma ta dauki kofin sau biyar sai Brazil ke biye da kofuna 3,

ADVERTISEMENT

Tuni Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aika da sakon taya murna ga Eaglets kan kokarin da suke yi a wannan gasa kuma ya nemi su ci gaba da zage damtse don ganin sun lashe kofin a karo na shida.

 

 

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya