✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

UAE ta janye takunkumin da ta sa wa Isra’ila

Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta janye soke alaka tsakaninta da Isra’ila sakamakon sasancin da Amurka ke jagoranto domin dawo da hulda tsakanin kasashen biyu ba…

Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta janye soke alaka tsakaninta da Isra’ila sakamakon sasancin da Amurka ke jagoranto domin dawo da hulda tsakanin kasashen biyu ba tare da togaciya ba.

A narar 13 ga Agusta ne aka sanar da kulla yarjejeniyar zaman lafiya da dawo da alaka tsakanin kasashen biyu. Yarjejejiyar na bukatar Isra’il ta dakatar da yunkurinta da mayar gabar West Bank karkashin ikonta.

A ranar Asabar gwamantin UAE ta fitar da dokar janye dukkannin nau’ikan kaurace wa Isra’aila, kamar yadda kamafnin dillancin labaru na AP ya ruwaito.

AFP ya ambaci kamfanin dillancin labaru mallakar gwamnatin UAE, WAM na cewa Sarkin Abu Dhabi kuma Shugban Kasar, Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan ne ya bayar da umarnin janye takunkumin.

Dokar ta ba wa Isra’ila da kamfanonin ’yan Isra’ila izinin yin kasuwanci a UEA. Ta kuma bayar da izinin saye da kuma kasuwancin kayan da aka sana’anta a Isra’ila a cikin kasar.

WAM ya ce, “Sabuwar daokar na daga cikin kokarin UAE da fadada huldar jakadancin da kasuwanci tsakaninta a Isra’ila”.

Ta kuma tsara “hanyar kula kawance da zai taimaka wa bunkasa tattalin arziki da kirkire-kirkiren fasaha”.