✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Uba ya banka wa dansa da ‘yarsa wuta saboda zargin maita

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta tabbatar da kama wani uba mai suna Nyam Choji da ke kauyen Shen a Karamar Hukumar Jos ta Kudu.…

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta tabbatar da kama wani uba mai suna Nyam Choji da ke kauyen Shen a Karamar Hukumar Jos ta Kudu. Saboda zargin banka wa dansa da ‘yarsa wuta akan zargin maita.

Mukaddashshin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ASP Uba Gabriel, ya tabbatarwa Aminiya kama mahaifin da ya kona ‘ya’yansa yaron mai suna Godsgift Nyam mai shekara 11 da kuma ‘yarsa mai suna Mary Nyam mai shekara , ya aikata hakan ne ranar Juma’a.