✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

United za ta ba Mourinho Naira biliyan 11 kudin sallama

Rahotanni da ke fitowa daga kulob din Manchester United sun nuna kulob din ya shirya don biyan diyyar Fam miliyan 24 (kimanin Naira biliyan 11…

Rahotanni da ke fitowa daga kulob din Manchester United sun nuna kulob din ya shirya don biyan diyyar Fam miliyan 24 (kimanin Naira biliyan 11 da miliyan 304) saboda sallamarsa da ta yi.  Za ta biya kudin ne a tsakanin kwana 45 bayan ta sallame shi.

Hakan ya biyo bayan yarjejeniyar da kocin ya kulla da United ne a watan Janairun bana, lokacin da aka sabunta masa kwantaragi zuwa shekarar 2020.

Yarjejeniyar ta nuna idan United ta sallami kocin kafin wa’adinsa ya kare, za ta biya shi diyyar Fam miliyan 24, kamar yadda shi ma zai biya kulob din wannan kudi idan ya ajiye aiki da kansa kafin karshen wa’adin nasa.  Kuma za a biya wannan kudi ne a tsakanin kwana 45 idan hakan ta faru, kamar yadda rahoton da kafar watsa labarai ta UK Sun ta kalato.

Kulob din Manchester United ya sallami Jose Mourinho ne a ranar Talatar da ta wuce, bayan ya kasa tabuka abin a-zo-a-gani a kakar wasa ta bana.

Mourinho wanda ya shafe shekara biyu da rabi a United, aikinsa ya zo karshe ne bayan kulob din Liberpool ya lallasa na United da ci 3-1 a gasar rukunin Firimiya ta Ingila a ranar Lahadin da ta wuce.

Rahoton da kafar labarai ta UK Sun ta kalato ya ce, rabon da kulob din United ya fuskanci irin wannan matsala tun shekara 28 da suka wuce.

Ganin yadda Mourinho ya  jefa kulob din a cikin matsala ta sa mahukunta kulob din suka yanke shawarar sallamarsa tun kafin ya kammala kwantaragin.

Mounrihon dai ya horar da kulob da dama da suka hada  Real Madrid da ke Sifen da Inter Milan na Italiya da Chelsea sau biyu sai kuma Manchester United.