Da Dumi Dumi

Uwargida ta tunkuda amarya a rijiya ta mutu

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano
Dr. Abdullahi Umar Ganduje

Al’ummar garin Rurum a Karamar Hukumar Rano a Jihar Kano sun wayi gari cikin alhini inda aka zargi wata mata mai suna Hauwa da kashe kishiyarta sakamkon tunkudata a rijiya da ta yi.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata da dare lokacin da marigayiyar wacce ke goye da danta dan kimanin shekara daya da watanni take kokarin dibar ruwa a rijiyar.

Mutanen unguwar sun yi gaggawar kai taimako inda suka yi kokarin fiddo da marigayiyar daga rijiya tare da danta, inda suka samu nasarar fitar da dan da ransa.

A ziyarar da Aminiya ta kai yankin Rurum ta gano cewa wannan magana ita ce ta zama abar tattaunawa a duk wani majalisi na al’ummar yankin.

Rahotanni sun ce akwai tsama tsakanin uwargida Hauwa da amaryarta marigayiya Zuwaira, lamarin da ya jawo uwargidan ta tunkuda ta cikin rijiya.

ADVERTISEMENT

Malama Binta Yakubu ita ce mahifiyar marigayiya Zuwaira ta ce a lokuta da dama marigayiyar tana korafi kan irin mummunan zaman da suke yi da abokiyar zamanta, sai dai ba su tava daukar wani mataki a kai ba, illa su rarrashe ta a kan ta yi hakuri.

Kakakin Rundunar ’yan sandan Jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin inda  ya  ce tuni wacce ake zargin ta amsa laifinta don haka ba tare da vata lokaci ba za a gurfanar da ita gaban kotu.

Wacce ake zargin da yanzu take tsare a ofishin ’yan sanda na Bompai ta ce marigayiyar ce ta kama ta da kokawa ta kuma shake ta a daidai lokacin da take dibar ruwa a rijiya, hakan ya sa ta hankada ta inda a karshe ta fada cikin rijiyar. “Rigima ce ta faru a tsakaninmu a ranar da lamarin ya faru. Ta je unguwa ta dawo da yake ni ke da girki, to na zuba mata abinci a kwanona sai na dauka na kai mata dakinta na ce ga abincinta, amma ko kallona ba ta yi ba. Sai kawai ta zubar da abincin ta dauki kwanon ta jefe ni da shi. Sai ni ma na dauki dutse na rama jifar. Daga nan sai na tafi ina dibar ruwa a rijiya, sai ta biyo ni ta kama ni da kokawa ta hada ni da jikin katanga ta shake ni. Da na rasa yadda zan yi in kwaci kaina sai na hankada ta, to da yake a bakin rijiya muke, shi ne ta fada ciki,” inji ta.

Ta kara da cewa, “Dama can ba mu zaman lafiya domin wannan ba shi ne karon farko da muka yi kokawa ba sau biyu tana kama ni da kokawa, a na biyun ma har gaban mai garinmu na kai kararta inda aka yi mana sulhu.”

Ta ce tsautsayi ne ya kai ta ga aikata laifin wanda kuma ta yi da-na-sanin aikata shi. “A gaskiya ban ji dadin abin da ya faru ba, domin ba haka na so ba. Ko akuya ba zan so in kashe ba, ballantana mutum. Da na san haka za ta faru wallahi koda namana take yanka ba zan kula ta ba,” inji uwargidan.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya