✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wadanda suka cancanci gwajin Coronavirus

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya ta yi kwaskwarima ga jadawalinta na ire-iren mutanen da suka cancanci a yi masu gwajin COVID-19. A…

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya ta yi kwaskwarima ga jadawalinta na ire-iren mutanen da suka cancanci a yi masu gwajin COVID-19.

A cewar hukumar, nau’in mutane uku ake yi wa gwaji a cibiyoyin gwajin da ta tanada.

“1. Matafiyan da suka dawo da zazzabi, ko tari, ko sarkewar numfashi;

“2. Wadanda suka yi mu’amala da mutanen da aka tabbatar sun nuna wadannan alamau;

“3. Masu fama da zazzabi da sarkewar numfashi kuma ba a san dalili ba a wuraren da ake da wadanda suka kamu da yawa ko daidai misali”.

A da dai ajin mutane biyu na farko kawai ake yiwa gwajin.

Hanyoyin gwajin

Hukumar ta ce mai son a yi masa gwajin sai ya dauki wasu matakai.

Na farko, ya tuntubi hukumomin lafiya na jihar da yake ko hukumar NCDC ta hanyoyin da aka tanada (layin wayar da ake tuntubar NCDC shi ne 080097000010 ko ta WhatsApp a 07087110839; yayin da jihohi suka tanadi nasu lambin wayar).

Mataki na biyu kuma shi ne mutum ya yi bayani dalla-dalla ga wanda ya amsa wayar game da abin da ke damunsa da alamomin da yake ji da kuma tafiye-tafiyen da ya yi.

Mataki na uku kuwa, inji NCDC, shi ne mutum ya zauna a gida ya saurari matakin da za ta dauka.

Ta kara da cewa za ta yi aiki da hukumomin jiha don daukar jinin wanda ke bukatar gwajin zuwa cibiyar da ta dace.

Cibiyoyin gwaji

Hukumar ta NCDC ta ce yanzu haka akwai cibiyoyi da ake yin gwajin a Najeriya, amma ana yunkurin kara yawansu.

Akwai cibiyoyi biyu a Jihar Legas, daya a Yankin Babban Birnin Tarayya, daya a Jihar Oyo, daya a Jihar Edo, daya kuma a Jihar Osun.

A na kuma aikin samar da wasu cibiyoyin a jihohin Sokoto da Filato da Borno da  Kano da Ebonyi da Ribas da Kaduna.