✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wadanda suka kamu da Coronavirus a Najeriya sun kai 70

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce an samu karin mutum biyar da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya. Wannan…

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce an samu karin mutum biyar da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya.

Wannan ya sa adadin mutanen da zuwa yanzu aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 70.

“Zuwa karfe 8:00 na daren ranar Juma’a 27 ga watan Maris, an tabbatar da karin mutum biyar sun kamu da COVID-19”, a cewar sanarwar da hukumar ta NCDC ta wallafa a shafinta na Twitter.

An dai samu karin mutanen ne a Yankin Babban Birnin Tarayya inda aka sanar karin mutum uku; sai kuma jihar Oyo inda aka samu mutum biyu.

A cikin mutum 70 din da aka tabbatar sun kamu da cutar an sallami mutum uku yayin da guda ya rasu.