✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wajibi ne a zakulo wadanda suka yi dalilin bacewar Janar Alkali – Jama’atu

A farkon wannan mako ne Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta Kasa ta kira taron manema labarai don nuna bacin ranta kan maganganun da wadansu shugabannin…

A farkon wannan mako ne Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta Kasa ta kira taron manema labarai don nuna bacin ranta kan maganganun da wadansu shugabannin addini da na jama’a suke yi kan bacewar Janar I.M. Alkali wanda aka gano motarsa a kududdufin Du da ke Jos a Jihar Filato. Aminiya ta tattauna da Babban Sakataren Dokta Khalid Abubakar Aliyu inda ya ce bai kamata shugabannin jama’a su rika kalaman tunzura jama’a ba. Kuma ya bukaci lallai a zakulo wadanda suka yi dalilin bacewar Janar din tare da bincikar daukacin kududdufan da suke yankin Du da Riyom:

Aminiya: Mene ne makasudin kiran taron ’yan jarida da kuka yi?

Mun kira taron ne don mu yi tsokaci kana bin da ya faru a Jihar Filato na bacewar Janar Idris Muhammad Alkali a kauyen Du. Gaskiya ba mu son a ce muna jayayya da Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a kan duk wannan batu ko kuma shi kansa Sanata Jonah Jang wato tsohon Gwamnan Jihar Filato. Amma abin bakin ciki ne a ce duk da kashe-kashen da ake yi a Jos ra’ayinsu a kan batun babu dadi, idan aka yi la’akari da irin kalamansu. Ba don sun fadi wasu kalamai marasa dadi ba da Jama’atu Nasril Islam ba za ta ce komai ba illa kawai ta yi kira ga Musulmin Jos su kwantar da hankalinsu.

Muna ganin cewa irin kalamansu na batanci da nuna kiyayya ne, amma ba ra’ayin mafi yawan Kiristocin Najeriya ba ne saboda akwai Kiristoci na kwarai masu son zaman lafiya a kasar nan. Wadanda ke kokarin furta kalamai masu kyau a lokacin da suka samu damar yin haka.

Wasu irin kalamai suka yi da ba su yi muku dadi ba?

Misali cewa wai hadari ne a bar wa Shugaban Buhari harkar tsaron kasar da Jonah Jang ya ce. Koda yake ba muna magana da yawun gwamnati ba ne amma wannan kalami bai dace ba, kuma kokari ne na batanci tare da kawo rashin yarda a tsakanin manyan hafsoshin soji musamman a matsayinsa na tsohon soja. Kalamansa na nufin jawo rikici da rashin kwanciyar hankali.

Ba mu ga laifinsa ba, laifin gwamnati muke gani da har ta bar mutane irin su suke wasu kalamai da ba su dace ba, ba tare da an hukunta su ba. Shi kuma Shugaban CAN na Kasa cewa ya yi wai an hallaka matasa da yawa saboda bacewar wani soja. To, bari mu fada masa cewa Manjo Janar I. M. Alkali, ya fi karfin a ce masa wani soja, domin mutum ne mai gaskiya da rikon amana wanda ya yi aikinsa cikin gaskiya na tsawon shekara 35. Babban jami’i ne a Rundunar Sojin Najeriya, saboda haka Shugaban CAN ya kamata ya iya bakinsa. Janar Alkali mutum ne mai kishinsa kasarsa kuma ga dukan alamu mun fahimci an hallaka shi.

Abin da ba mu sani ba shi ne ko Shugaban CAN yana magana ne da yawun wadanda suka aikata ta’asar? Ko kuma ya san inda Janar Alkali yake ne? Domin duk mai kishin kasa kamata ya yi ya nuna damuwa a kan abin da ya faru da wannan Janar na soja. Muna da yakinin cewa duk wanda ke da hannu a bacewar wannan Janar ba za su taba samun kwanciyar hankali ba, insha Allahu.

Kuma ina dalilin karairayin da al’ummar yankin da kuma CAN suke yi a kan bacewarsa. Me ya sa aka tura mata sama da 500 domin yin zanga zanaga a lokacin da ake kokarin yin bincike a kududdufin da ke garin Du? An nuna su a gidan talabijin na NTA, wannan ya nuna cewa suna sane da ta’asar da ake aikatawa a yankin. Domin masana a cikin soji sun fahinci hakan a lokacin zanga-zangar.

Jama’atu ta damu matuka a kan rikicin da ke faruwa a Jos da kewaye duk da kokari da ake yi na ganin jama’ar Jihar Filato sun zauna lafiya. Don haka muna Allah wadai da wannan lamari kuma muna jajanta wa duk wadanda suka rasa rayukansu a lokacin rikicin, muna addu’a wadanda suka samu raunaku su samu sauki

Ke nan kuna ganin akwai masu neman bata ruwa domin a ga kamar gwamnati ta gaza?

Kwarai kuwa akwai hakan, domin a nuna cewa Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Filato sun gaza. Baya ga haka Kungiyar Tsaro ta Operation Rainbow ba ta taka rawar gani ba domin sun taimaka wajen hallaka ’yan Najeriya, musamman Musulmi. A wannan rikici da aka yi a garin Jos mun fahimci sabon salo wajen kashe Musulmi ta hanyar bin gida-gida ana nuna Musulmi sannan sai a bace daga wajen.

Wadanne unguwanni abin ya shafa?

Unguwanin Dutse Uku da Rikkos da Unguwar Damusa da Ali Kazaure da Farar Gada da Naraguta da Katako da kewaye inda abin ya fi kamari ke nan Sannan an rufe su na tsawon sa’o’i 48.

Mu a Musulunci kisan wani dan Adam babban laifi ne kai ya ma fi ka rusa Ka’aba, da ka kashe Musulmi wannan ya sa muke ganin duk wanda ke da hannu wajen kashe-kashen nan dole a hukunta su.

Kuma muna ganin a duk inda aka ce an samu rikici irin haka kamata ya yi jami’an tsaro su yi amfani da doka wajen kwantar da tarzomar. Sai dai abin bakin ciki Musulmi abin ya fi shafa a duk lokacin da sojoji suka rufe wata unguwa ko gari. Saboda haka ya sa muke mamakin yadda sojoji suke yi wa garin Du inda aka gano wannan kududdufi rikon tsakainar kashi. Duk kuwa da an gano wannan mugun kududdufi da ake jefa mutane bayan an kashe su.  Mun samu labarin cewa ba ya ga motar Janar Alkali an gano wasu mutoci a cikin kududdufin da suka hada da bas ta Jihar Gombe da wasu motoci Toyota Hiace bas da Bolbo da babura da Keke NAPEP da wasu gawarwaki. Ga alama babu tausayi a zukatan al’ummar yanki babu yadda za a kasance muna da addini amma ba mu da tausayi.

Abin mamaki duk da kasancewar an gano wannan kududdufi a Du kungiyoyin kare hakkin dan Adam na cikin gida Najeriya da na kasashen waje duk sun yi shiru ba su ce komai ba. Da a ce a garin Musulmi aka samu wannan kuddudufi kuma ana kashe Kiristoci a jefa da an bani da surutansu. Su ma mafi yawan kafafen watsa labarai na gida da na waje sun ki cewa komai a kan gano wannan kuddufi wanda hakan ke nuna munafunci karara.

Kwanakin baya mun ga yadda wasu kafafen watsa labarai suka ki mayar da hankali a kan kokari da Imam Abdullahi Abubakar da ke kauyen Nghar a Gundumar Gashish a Karamar Hukumar Barikin Ladi, ya yi waje ceto Kiristoci 300 daga mahara. Da a ce Fasto ne ya yi haka da an yi bikinsa fiye da yadda ba a tsammani.

Yanzu me Jama’atu take so?

Jama’atu tana kira ga Gwamnatin Tarayya cewa bisa adalci da neman zaman lafiya da fahimtar juna ta kafa kwamiti mai karfi da zai binciki abin da ke janyo rikici tare da gano hanyoyin magance su. Ya kamata gwamnati ta wuce zancen yin Allah wadai kurum dole ta rika daukar matakin mai do da zaman lafiya musamman a garuruwan da abin ke shafa.

Muna kuma kira ga gwamnati da sojoji da kada su yi kasa a gwiwa wajen gano inda Manjo Janar Alkali yake kuma duk wanda aka samu da hannu a bacewarsa a hukunta shi komai matsayinsa. Muna fatan al’ummar Filato za su ba da goyon baya dangane da bincike da Rundunar Soji ke yi a yankin.

Muna fatan gwamnati ta hukunta makiya zaman lafiya a yankin musamman masu hura wutar kabilanci da kiyayya a tsakanin jama’a. Ita ma gwamnatin Filato muna son ta tashi tsaye wajen kawo karshen wadannan fitinu a jihar. Sannan dukan kududdufan da suke yakin Lafendeng da Dura Du da wadanda ke kusa da Riyom da Heipang da Kassa a Barikin Ladi a binciki abin da ke cikinsu. Domin ’yan Najieriya za su yi matukar mamakin abin da kila za a gano a ciki. Sannan muna kira ga jami’an tsaro su kawar da da son zuciya wajen gudanar da aikin.