✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wajibi ne gwamnati ta hana sare itatuwa – Dokta Abubakar Hassan

Dokta Abubakar Abdullahi Hassan, shi ne Shugaban Sashen Noma na Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, rashen Mando, Kaduna ya zanta da Aminiya a wajen taron koyar…

Dokta Abubakar Abdullahi Hassan, shi ne Shugaban Sashen Noma na Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, rashen Mando, Kaduna ya zanta da Aminiya a wajen taron koyar da matasa 200 sana’ar kiwon kifi da dashen itatuwa da Gonar Teku Farm ta shirya a Kaduna. Malamin ya bukaci gwamnati ta tashi tsaye wajen hukunta masu sare itatuwa a dazuzzuka:

Me za ka ce game da batun sare itatuwa da wadansu ke yi; wanda hakan ke janyo hamada a kasar nan?

A gaskiya muna cikin wani mugum hali a yanzu saboda idan muka yi wasa wannan gurgusowar hamada da ke faruwa a yanzu za ta iya kawo lokacin da za a daina samun ruwa. Haka kuma za ta iya kawo ambaliyar ruwa inda ko da ma mun yi shuka ba zai amfane mu ba domin duk inda ruwa ya yi wa shuka yawa ba zai yi ba. Saboda matsalar gurgusowar hamada na kawo karanci ko yawan ruwan sama. Shi ya sa za ka ga wani wuri da a da ba a samun ruwa; amma a yanzu sai ruwa ya cika muku waje har ya cinye gonaki da gidaje. Idan ruwa ya ci gonaki ka ga an samu matsala ke nan.

Saboda haka wadannan masu Gonar Teku da suka koya wa matasan sana’ar kiwo da dashen itatuwa abin a yaba musu ne; kuma gaskiya akwai bukatar gwamnati ta tallafa musu, wannan zai taimaka wa yanayi.

Daya daga cikin matsalolin gusowar hamada shi ne sanya mutane yin hijira, dabbobi kuma na canja wurin zama. Yaya kuke kallon wannan lamari?

Gaskiya dai wannan babbar matsala ce; wadda a gaskiya dole sai gwamnati ta tashi tsaye. A yi duk yadda za a yi, a ga an hana mutane sare itatuwa da  kona tayoyi da mutane ke yi wanda duk bai dace ba. Yanzu haka idan ka je wuraren Panteka za ka ga ana ta kona taya ko’ina wanda kuma yana da mugun illa a kan yanayi kuma duk hakan ke kawo matsaloli.

Duk da muna da Ma’aikatar Kula da Muhalli amma kusan ba su yin komai akan batun nan. Na koka a kan wannan abin; amma har yanzu sun kasa hanawa. Saboda kawai a cire wata waya a taya amma sai a jefa miliyoyin mutane cikin matsala. Dole ne gwamnati ta tashi tsaye ta hana kona taya da ake yi a cikin al’umma.

Akwai masu ganin dazuzzukan Nahiyar Afirka na cikin matsala saboda sare itatuwa; ko za ka yi mana karin bayani?

Babban matsalar ita ce, sassare itatuwa da ake yi ana amfani da su wurin girke-girke. Gwamnati za ta iya fito da hanyoyin da ba lallai ba ne sai an yi amfani da itace ba. Akwai hanyoyi da yawa da gwamnatin da ta gabata ta zo ta yi amfani da su; amma saboda rashin gaskiyar mutane an kashe kudi amma ba a yi ba. Sai dai kawai mu yi addu’ar Allah Ya sa wadanda ke kan mulki a yanzu su zo su yi abin da ya kamata domin mu kwaci kanmu.

Da zarar fa aka ce babu ruwa ko kuma an fara ambaliya ko a ce babu abinci an shiga uku; domin abinci shi ne mutane. Ana iya wahalar man mota mutane su ci gaba da rayuwa amma da zarar an ce maka babu abinci to akwai matsala.

Me za ka ce game da dabbobin da ake babbakewa da tayar mota?

Ka ga wannan ma fa babbar matsala ce domin wannan tayar tana dauke da sinadiran da suke kawo cutar daji wato kansa. Sannan ka zo ka kona kan dabba da shi sinadirin ya shiga cikin nama; ka kuma je ka raba wa mutane. Shi ya sa ake  ta samun yawan masu cutar daji a yanzu. Ba sai mutum ya tsufa ba; domin sai ka ga yaro karami an same shi da cutar daji. Duk wannan abin ne ke kawo shi; saboda haka dole gwamnati ta hana, in ba haka ba kuwa al’umma na cikin matsala.