✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani fim din badala ya haifar da cece-cece ku ce

Sunanta Judith Opara amma an fi saninta da lakanin ‘Afrocandy.’ Ita haifaffar Najeriya ce, wacce ta yi rayuwarta a Amurka. Ta kasance mawakiya, ’yar fim…

Sunanta Judith Opara amma an fi saninta da lakanin ‘Afrocandy.’ Ita haifaffar Najeriya ce, wacce ta yi rayuwarta a Amurka. Ta kasance mawakiya, ’yar fim kuma furodusa.
A yayin da abokan sana’arta ke shirya fina-finan kwarai, ita ta fi kwarewa wajen shirya fina-finan badala, domin kuwa ko a watan jiya ta yi bikin gabatar da wani sabon la’antaccen fim din da ta shirya, na badala.
A ’yan kwanakin nan ne ta shiga tsomomuwa, inda wani fim da ta shirya na badala, wanda kuma bai kai ga fitowa ba ya haifar mata da cece-kuce, tsakaninta da dan was an da ya amince ya jagoranci fim din.
Kamar yadda ’yar fim din ta bara da bakinta a turakarta ta Facebook, ta ce wani dan wasa yana neman jika mata aiki, inda ya yi mata gargadin lallai ta yi hanzarin cire tallar fim din na badala daga shafukan intanet.
Kamar yadda al’amarin ya faru, Afrocandy ta dauki hayar wani dan fim ne, ta biya shi makudan kudi, ta shaida masa cewa fim din badala za su shirya kuma ya amince. Sun dauki fim din kuwa, mai cike da hotunan tsiraici da badala. Ta yi murna sosai, tana shirin fitar da shi kasuwa, ta fara tallata shi a yanar gizo, sai wannan dan fim ya fara yi mata barazana cewa lallai ne ta dakatar da sanya tallar fim din, domin kuwa iyayensa da budurwarsa sun harzuka kuma za su la’ance shi.
“Ku gane mini wannan dan wasa, na biya shi kudi masu yawa, mun yi yarjejeniya cewa fim din badala za mu shirya. Mun shirya fim din, amma ganin cewa na fara tallata hajata, shi kuma yana cewa lallai ne in cire shi daga fim din, yana yi mani barazana, kawai wai domin iyayensa da ’yan uwansa da budurwarsa sun kore shi daga jikinsu. Shin yaya yake so in yi da kudin da na kashe?” Inji Afrocandy.