✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani tsagin APC ya sake dakatar da Ganduje

Sarina ya ce har yanzu wannan batu na masu shigar burtu ne da nufin yaudara.

Rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar APC a Jihar Kano ya sake ɗaukar sabon salo, a daidai lokacin da wani tsagin da ya fito daga Mazaɓar Ganduje, ya sake dakatar da Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

A makon da ya gabata ne wani tsagin shugabannin jam’iyyar da ke mazaɓar tsohon Gwamnan Kanon ƙarƙashin jagorancin Haladu Gwanjo ya dakatar da Ganduje.

Da yake bayyana zargin cin hanci da rashawa da dai sauran laifuffuka, Gwanjo ya ce mambobin jam’iyyar tara ne suka yanke shawarar dakatar da tsohon gwamnan Kano a mazaɓar Ganduje.

Sai dai wani tsagin da Ahmad Ganduje ya wakilta ya fito ya bayyana goyon bayansa ga shugaban jam’iyyar na ƙasa, inda ya jaddada cewa jami’an mazaɓun sun gamsu da salon shugabancinsa.

A yayin da lamarin ya ɗauki sabon salo, tsagin ƙarƙashin jagorancin sakataren mazaɓar, Jaafar Adamu ya bayyana wa manema labarai a ranar Lahadin nan cewa 11 daga cikin 27 na ƙaramar hukumar Ganduje sun kasance halastattun jiga-jigan jam’iyyar da aka zaɓa a ranar 31 ga Yuli, 2021.

Jaafar wanda kuma ƙani ne ga Ganduje ya ce, “Mu ne nagartattun shugabannin mazaɓar Ganduje kuma mun kaɗa ƙuri’ar ƙin amincewa kuma muka sanya wa Dakta Umar Ganduje sabuwar dakatarwa saboda wasu dalilai.

“Da farko mun dakatar da Dakta Ganduje daga cikin mambobin jam’iyyar saboda haifar da rikicin cikin gida a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar a matakin mazaɓu.

“Wani babban dalilin ne da ya sa halastattun shugabannin zartarwa suka yanke shawarar dakatar da Ganduje, shi ne batun ayyukan cin hanci da rashawa da ya haifar a lokacin zaɓen 2023, wanda ya nuna gazawar jam’iyyar a jihar.”

APC ta yi martani

Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta sake bayyana dakatarwar da aka yi wa shugaban jam’iyyar na kasa a baya-bayan nan a matsayin wani lamari na yaudara.

Sakataren jam’iyyar a jihar Ibrahim Zakari Sarina ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da wakilinmu ta wayar tarho.

Sarina ya ce har yanzu wannan batu na masu shigar burtu ne da nufin yaudara amma ba halastattun shugabanni ba ne a mazabar Ganduje.

Duk da cewa ya amince halascin kasancewa ’ya’yan jam’iyya daga cikin masu ikirarin dakatar da Ganduje a matakin mazaba, sai dai ya ce su ba shuwagabanni ba ne kuma ba su da wani mukami a jam’iyyar a kowane mataki.

“Wasu daga cikinsu ‘ya’yan jam’iyyar APC ne amma ba su taɓa zama shugabannin zartarwa ba kuma ba su taɓa riƙe wani mukami ba. Hatta wanda aka ce shi shugaba a mazabar bai taɓa zama cikin masu zartarwa ba.”

Sarina ya kara da cewa jam’iyyar a jihar na kokarin ganin ta tabbatar da shugabannin jam’iyyar na gaskiya nan ba da jimawa ba.