Da Dumi Dumi

…Wata kuma ta yi garkuwa da mai neman aurenta kwana biyu kafin a yi bikinsu

Wata mata ta yi ikirarin  yin garkuwa da mai neman aurenta lokacin da ya rage kwan a biyu a daura musu aure, kamar yadda shafin sadarwar Dillancin labarai na kasar Saudiyya sabk ya ruwaito.

Amaryar da aka so daura mata aure da angonta mai shekara 48, ta kira shi ya zo su gana da iyayenta don karkare tsare-tsaren biki da kudin da za a kashe a wajen bikin.

Daidai lokacin da ya tunkari gidansu, sai wasu maza suka tare shi, inda suka jawo shi daga cikin mota, suka lalube shi, suka dauke riyal dubu 20, sannan suka kai shi wani wuri suka boye.

“daya daga cikin wadan da suka sace mutumin dogo ne, sanye da lullubin fuska, shi kuwa dayan ya daure fuskarsa ne da rawani,” kamar yadda manemin auren ya bayyana wa ’yan sanda.

ADVERTISEMENT

A cewarsa: “sun daure hannayena, suka kai ni wani kebabben wuri, inda suka tube ni, suka dauki hotuna na.”

Da farko matar ta karyata cewa tana da hannu a lamarin, amma da ’yan uwan ta suka yi ikrarin abin da suka kulla a gaban ’yan sanda, sai ta ce ta yi hakan ne don ba ta son auren mutumin,” al’amarin da ke nuni da cewa iyayenta ne suka tursasata ne ta yi wannan auren.

Mutane biyun da ’yan sanda ke tsare da su, daya mai shekara 21, dayan kuwa mai shekara 27. A halin yanzu suna jiran a gurfanar da su a kotu.

Wannan mata dai tuni wata kungiya mai kula da tarbiyyar mata da ke da gida a birnin Makkah ta dauketa kafin a kammala bincike kan lamarin.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya