✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata sabuwar cuta ta bulla a Legas

Gwamnatin Jihar Legas ta gargadi mazauna jihar su yi taka-tsantsan wajen yin musabaha da jama’a don gudun kamuwa da wata sabuwar cuta da ta bulla…

Gwamnatin Jihar Legas ta gargadi mazauna jihar su yi taka-tsantsan wajen yin musabaha da jama’a don gudun kamuwa da wata sabuwar cuta da ta bulla a jihar mai suna Coronabirus.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dokta Jide Idris, wanda ya yi gargadin lokacin da yake ganawa da manema labarai a farkon makon nan ya ce ana kamuwa da cutar daga wanda yake dauke da ita cikin sauri.
Ya ce, “Mutum zai iya kamuwa da cutar ta hanyar tari ko atishawa ko kuma hada jiki da mai dauke da cutar ko ma ta hanyar yin musabaha da shi ko ta hanyar taba hanci ko baki ko idon mai dauke da cutar ko kuma yin amfani da wani abu da mai dauke da ita ya yi amfani da shi”.
Ya bayyana cewa cutar ta Coronabirus takan fara ne da zazzabi dan kadan daga bisani sai zazzabin ya rika karuwa, sannan takan haifar da cutar sanyi ta numoniya ga wadanda suka kamu da ita.
Ya kara da cewa cutar takan kama kowane jinsi na mutane, kamar yara da matasa da kuma tsofaffi. “Har yanzu babu takamaiman maganin cutar. Da yawa wadanda suka kamu da ita sukan iya warkewa da kansu ba tare da shan magani ba, amma sau da dama wadanda suka kamu da ita sukan bukaci a taimaka musu da agajin gaggawa kamar hutawa a gida da shan magungunan da za su kara musu ruwa a jiki. Wadanda cutar ta yi musu tsanani kuwa dole a kai su asibiti cikin gaggawa”. Inji shi.
Dokta Idris ya kara da cewa za a iya rage hadarin kamuwa da cutar idan mutane suka kiyaye tsaftace muhallinsu da wanke hannayensu da sabulu da kuma guje wa taba idanu da baki da hanci da nisantar marasa lafiya da cunkoson jama’a da kuma tsaftace abubuwan da mai dauke da cutar ya yi amfani da su.