✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wutar lantarki ginshiki ne na tattalin arzikin kasa – Ministan Makamashi

A tattaunawar da Aminiya tayi da Ministan Makamashi Injiniya Sale Mamman, ya bayyana cewa babu kasar da zata ci gaba idan babu wutar lantarki, idan…

A tattaunawar da Aminiya tayi da Ministan Makamashi Injiniya Sale Mamman, ya bayyana cewa babu kasar da zata ci gaba idan babu wutar lantarki, idan an same ta kasa zata wadatu kuma za a samu ci gaba. Wutar lantarki shi ne komai. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Me kake a kai?

Kamar yadda ka ce, in Allah Ya yarda Shugaba Buhari ba zai kammala wa’adinsa na biyu ba, sai an fara wannan aikin na Mammbila, tunda yake an dan samu jinkiri zai kasance baza a kammala a wa’adinmu ba, za a ci karfin aikin tunda masu bamu filin sun yi an gama komai.

Mun yi magana ga Gwamnan jihar ya yarda ya ce muje muyi aikin lantarkin mu, mun bada kudi munje mun auna kuma mun  ba masu aikin aunawar kudinsu hannu cewa, ga shi kuje ku rike a hannunku. Wannan shi ne tabbas harkar Mambila ya zama gaskiya, babu karya a cikinsa in Allah Ya yarda.

Farawan shi ne wuya, karka manta kudi ne. Kashi 85 cikin 100 na kudin  za a bamu ne daga waje ne, kashi 15 cikin 100 ne zamu bayar to idan har an fara bada kudi ne a kasa sunansa an gama.

Abin da yasa ba a fara da wuri ba, Allah ne kadai ya sani akwai harkar kotu a ciki wani yana cewa shi ne aka ba kwangilar, wasu kamfani suka ce su aka ba, damme ba a ba shi ba? Irin wadannan ke jawo abubuwan. A  tsaya a yi maganinsa ba a samu an yi ba, sai wannan karon ne muka ce, a tsaya a yi maganin abun.

Amma kun daidaita da su?

Mun daidaita, muna kan magana har yanzu, Insha Allahu zamu daidaita. Ina so in tabbatar maku da cewa, wannan aikin ba zai tsaya ba. Za a fara kamar yadda muka ce za a fara. Kuma babu kotun da tace kadda mu fara wannan aikin, an gama maganar  sun fahimce mu, har mun basu tabbas, ku zo mu fara duk abin da ya faru daku mun dauki nauyi mun yadda.

Za ku biya diyya?

Yanzu haka kudin diyya ya fita, na rubutawa shugaban kasa ya sa hannu, kudin diyya ya fita kudin auna fili ya fita.

Saura a fara aiki kenan?

Yanzu sun ce na basu wata daya zuwa biyu kafin su gama aune-aunen , masu biya ma zasu zo suma zasu dauki wata daya kafin nan kamfani zaizo, shi kenan a warware komai, sannan zasu zo a fara kawo kaya, za a gyara wurare kamar hanya.

A zagaye-zagayen da ka yi zuwa su Kashimbila da Zungeru, me ka gano?

Eh, sunan suna aiki awa 24 komai na ta tafiya, sun kai sama da rabin aikin kusan kashi 65 cikin 100, sun yi nisa sosai insha Allah cikin wannan shekarar zuwa karshenta abin da suka tabbatar mana kenan, idan kaje ka gani suna aiki awa 24 kamar yadda na fadamaka.

Dan adam na aiki sama da dubu biyu a wajen, idan kaje Zungeru kuma an riga an karasa, idan kaje wasu wuraren anan akan hanya. Duk an yi nisa sai kaddamarwa ya rage a yi, wuta zamu samu isasshe don haka muka ce kafin wannan gwamnatin ta sauka. Shi yasa muka ce idan an kammala aikin gyaran da rarraba wutar lantarkin za a samu wadatar wuta.