Search
Subscribe
Ya bukaci shugabanni su guji nuna isa da girman kai

Ya bukaci shugabanni su guji nuna isa da girman kai

Babban Limamin Masallacin Juma’a na hanyar Kano da ke Damaturu a Jihar Yobe Ustaz Babagana Malam Kyari ya bukaci shugabanni da malaman addini da masu hannu da shuni su guji nuna isa da kuma girman kai saboda babu abin da za su haifar ga mai aikata su face aukawa cikin halaka.
 Ustaz Babagana Malam Kyari ya yi wannan kira ne nasihar da ya ya saba yi a ranar Juma’a, inda ya ce aksarin shugabanni musamman masu rike da mukaman gwamnati da na siyasa da masu hannu da shuni na kokarin shiga mulkin Allah ta wajen nuna cewa abu kaza da kaza ba za su yiwu ba, face da hannunsu ta yadda in ba su suka yunkura ba, babu abin da zai  iya samuwa kuma koda wani matsayi wani ke nema sukan ce in har ba su sa hannu ga mai neman ba, to kuwa ba za a kai ga nasara ba!
 Ustaz Babagana ya ci gaba da cewa Allah Ya ce, koda daidai da kwayar zarra mutum ya je maSa da burbushin jiji da kai ko girman kai a cikin zuciyarsa a ranar Lahira ba  zai shiga Aljanna ba.
 Malamin ya kara da cewa a wani sahihin Hadisi daga Abu Huraira Manzon Allah (SAW) ya ce mutum uku ba za su shiga Aljanna ba, shugaba azzalumi da talaka da mai girman kai da mai dukiyar da ba ya fidda zakka.
 Don haka ya gargadi shugabanni da ’yan siyasa su guji fadin cewa, in ba tare da tallafinsu ba babu wani wanda ya isa ya kai ga wata bukatarsa in ma ta neman wani matsayi ko kuma kan abin da ya shafi harkokin dukiya da sauransu.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin