Da Dumi Dumi

Ya dace a hana daukar hoto da bidiyo a wajen kada kuri’a?

Sam bai dace a hana ba – Ahmadu A.  Is’hak

Daga Aliyu Babankarfi, Zariya

Ahmadu A. Ishak: “A gaskiya duk wani mataki na hana daukar hoto ko bidiyo a wajen kada kuri’a sam bai dace ba, domin matakin da aka dauka ba zai rasa nasaba da ganin cewa an inganta tsarin ba. To in ka auna da hanawar, illar da za ta yi  ya fi na barin. Misali,  a yanzu ’yan jarida da me suke amfani, kuma ba lallai ne ba idan na je na dauko labarina ko na dauko hotona in fallasa wa duniya kafin in samu yadda  zan yi, domin a kan tafiyar da ake ma ’yan jarida yanzu na neman su kawo huja to halin yaya. Kuma ka ga daukar hoto na daya daga cikin hujjojin ’yan jarida. Haka akwai wanda ba dan jarida ba, amma zai ga abu wanda wannan abin muhimmi ne kuma ba ’yan jarida a wurin, kuma ya dauka ya baza kuma ya amfani al’umma. Ka ga ai ya taimaki al’umma. Don haka ba na goyan bayan hanawa.”

Hanawar ta dace saboda matsalar da hakan ke haifarwa –Farfesa Mariyatu Tanoce

Daga Aliyu Babankarfi, Zariya

ADVERTISEMENT

Farfesa Mariyatu Tanoce da ke tsangayar koyar da kimiyyar siyasa a Jami’ar Jihar Kogi ta ce, “Ina goyon bayan hanawa saboda matsalar da hakan ke haifar wa na yin amfani da damar wajen ruda al’amura. Don haka ina goyon bayan a hana daukar duk wani hoto ko bidiyo a lokacin kada kuri’a ko a wajen fadin sakamakon zabe domin rudanin da hakan ke haifarwa. Hakan zai taimaka wajen samar da natsuwa da gudun tashin hankali da hakan ke iya haifarwa. Don haka ina goyon bayan hanawa.”

Bai dace a hana ba –Abubakar Salisu

Daga Lubabatu I. Garba, Kano

Abubakar Salisu: “A ra’ayina bai kamata a hana ba saboda daukar hotunan musammam yadda ake watsawa a kafafen sada zumunta ta Intanet zai sa mutane su ki aikata magudi. Amma idan mutane suka san an hana daukar hotuna to hakan zai ba su damar gudanar da magudi ba tare da jin tsoron za a dauki hotonsu ba.”

Hanawar ta dace – Mansur Abubakar 

Daga Lubabatu I. Garba, Kano

Mansur Abubakar: “Ni a ra’ayina ya kamata a hana saboda a wasu lokuta mutane suna daukar hotunan amma idan sun tashi tura hotunan a kafafen sadarwa sai su canja  ainihin hoton. Ma’ana ana amfani da hotunan ne ba a lokacin da aka dauke su ba. Hakan ya faru a zaben kananan hukumomin Jihar Kano da aka yi kwanakin baya inda aka rika tura wani hoton yara masu karancin shekaru suna kada kuri’a. Lokacin da aka bincika sai aka gano ba a wannan lokacin aka yi hoton ba.”

Ci gaba ne a rika daukar hoton – Auwal Sagir

Daga Isiyaku Muhammed

Auwal Sagir: “A nawa ra’ayin bai kamata a hana daukar hoto a wajen kada kuri’a ba domin kamar an dakatar da wani ci gaba ne da muka fara samu. Idan ana kada kuri’a, sannan aka yi magudi, za a iya daukar hoto a yada wanda kuma hakan zai zama hujja wajen kai karar wadanda suka yi magudin. Don haka ba na goyon bayan a hana.”

Bai kamata ba – Gwani Mukhtar

Daga Isiyaku Muhammed

Gwani Mukhtar Abdullahi: “Me zai sa a hana dauka? Sai dai idan an shirya magudi a boye, kuma ba a so a yada wa duniya su gani. Wannan wani ci gaba ne aka samu wanda zai iya taimakawa wajen magance magudi.”

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya