✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya dace a sanya dokar ta baci a Jihar Zamfara

A daidai lokacin da ake ci gaba cece-kuce kan kashe-kashen da ya addabi Jihar Zamfara da ta yi fice kan satar mutane da dabbobi, mutane…

A daidai lokacin da ake ci gaba cece-kuce kan kashe-kashen da ya addabi Jihar Zamfara da ta yi fice kan satar mutane da dabbobi, mutane suna ta kira ga gwamnati ta kara kaimi wajen shawo kan lamarin. Daga kiraye-kirayen da mutane suka yi, akwai maganar a sanya dokar ta-baci a jihar. Wannan ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin ra’ayoyin mutane, kuma ga abin da suke fada:

 

Na goyi bayan a sanya dokar ta-baci – Sa’adatu M. Hussain

Ahmed Garba Mohammed a Kaduna

Sa’adatu M. Hussain: Ina goyon bayan a kafa dokar ta-baci dari bisa dari a Jihar Zamfara ganin yadda ake yawan samun kashe-kashen bayin Allah da yin garkuwa da su ana karbar kudin fansa. A kullum sai ka ji an kashe wani ko wadansu ko kuma an yi garkuwa da wani ko wadansu. Abin tambaya a nan  ina gwamnati take?

Kamar yadda Hausawa ne ke cewa “Ba gagararre sai bararre.”  Don haka ina ganin idan aka sanya dokar ta-baci a jihar za a shawo kan matsalar cikin kankanen lokaci.

 

Ina goyon baya – Alhaji Sani Jatau

Daga Nasiru Bello, Sakkwato

Alhaji Sani Jatau: ‘Ina goyon bayan a sanya dokar ta-baci dari bisa dari tunda ko Gwamnan da yake mulkin jihar ya goyi bayan saka dokar. Mu talakawa duk yadda muke ganin mun san lamari, ba za mu kai mai mulki ba kamar yadda Hausawa ke cewa mai daki shi ya san inda yake zubar da ruwa. A gaskiya Gwamnatin Tarayya in da gaske take, abu ne mai kyau bukatar yin hakan. A lokacin da Obasanjo ya saka dokar ta-baci a Filato, an ga amfaninta da gudunmawar da aka samu a harkar tsaron jihar domin kowa ya san tsaro ya inganta a lokacin kafin abu ya koma baya. Don haka na goyi baya kuma abu ne da mafi yawan Zamfarawa ke so don wannan hali na kashe-kashe ya ishe su.”

 

Ya dace a sanya dokar – Dauda Usman Miko

Daga Aliyu Babankarfi, Zariya

Dauda Miko, dalibi a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria: “Ya dace Gwamnatin Tarayya ta sanya dokar ta-baci a Jihar Zamfara saboda da ta samu saukin samar da tsaro a jihar, kasancewar ana zargin mafi yawa daga cikin masu mulki da sarakuna suna sakaci da batun tsaron da ke haddasa asarar rasa rayuka da dukiyoyin al’umma. Don haka tsame hannun masu rike da madafun iko da  masarautun gargajiya zai taimaka.”

 

Sanya dokar zai fi dacewa  – A’isha Abubakar

Ahmed Garba Mohammed a Kaduna

A’isha Abubakar: A gaskiya idan ba a dauki matakin gaggawa wajen sanya dokar ta-baci a Jihar Zamfara ba, to hakan zai iya watsuwa zuwa wasu jihohi na Arewa.  Dalilin kuwa shi ne yadda gwamnatin Jihar Zamfara ta yi biris da daukar matakin magance wannan matsala ta kashe-kashen al’umma babu gaira, babu dalili. Hakan zai ba batagarin damar shiga sauran jihohi makwabta tunda wadanda ke zaune a Zamafa kullum sai kaura suke yi zuwa wasu jihohi.

Sannan ganin yadda shi kansa Gwamnan Jihar Zamfara Abdul’aziz Yari ya amince a kafa dokar ta-baci a jihar ya nuna ba zai iya shawo kan matsalar ba, don haka abin da ya fi dacewa shi ne a kafa dokar ta-baci ba tare da bata lokaci ba.”

 

Ya kamata a sanya dokar – Haliru Bara’u Dankawu

Daga Nasiru Bello, Sakkwato

Haliru Bara’u Dankawu: “Dokar ya kamata a sanya tuntuni domin al’umma sun shiga hali kunci da rashin tabbas. Muna ganin in an karbe karfin ikon tafiyar da gwamnati daga  Gwamnan da ke ci yanzu ana iya samun saukin halin da ake ciki na kashe-kashe da garkuwa da mutane. Duk da lokacin siyasa ne yanzu kuma akwai tsammanin canja gwamnati a jihar, yin dokar abin maraba ne ga kowa don ba wanda ke son jin dan uwansa a cikin kunci ko na minti daya ne ballantana na kwana daya ko fiye. A sanya dokar ta-baci domin mafi yawanmu masu kishin kasar nan da Arewa muna son jin matsalar Zamfara ta zama tarihi.”

 

Ina goyon bayan sanya dokar ta baci a Zamfara – Ahmad Garba Tudun Jukun

Daga Aliyu Babankarfi, Zariya

Ahmad Garba Tudun Jukun: “A ra’ayina ya dace gwamnati ta sanya dokar ta-baci saboda halin da mutanen Zamfara ke ciki na firgici da rasa rayuka da dukiyoyi ga kuma zabe yana kara kusantowa. Don haka sanya dokar ta-baci kadai ne zai samar da yanayi mai kyau har a samu damar gudanar da zabe sahihi saboda rashin yarda da talakawan ke wa masu rike da madafun iko a jihar. Don haka ina goyon bayan sanya dokar ta-baci don al’ummar jihar su samu natsuwa.”