✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya hallaka mahaifiyarsa mai shekara 70 a Akwa Ibom

’Yan sanda sun bayyana damuwa kan yawaitar laifukan kisa yayin da kwanan nan wani ya kashe ɗansa.

Wani mai suna Inyagake ya kashe mahaifiyarsa mai shekara 70 a Jihar Akwa Ibom.

Mutumin mai shekara 40 ya hallaka mahaifiyarsa mai suna Mma Effiong James Peter ne a cikin ruwan sanyi.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Ikpe Annang da ke Ƙaramar Hukumar Essien Udim ta jihar da misalin ƙarfe 9 na safe.

Hakan dai ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, CSP Odiko Macdon, ya fitar a ranar Litinin da ta gabata.

Kakakin ya ce, wanda ake zargin ya shiga hannunsu kuma ya amsa laifinsa inda ya ce ya yi haka ne bisa umarnin wata murya da ya ji da take umartarsa da ya hallaka mahaifiyar tasa kuma ya aikata.

Ya ce, “Wanda ake zargin ya amsa laifin kuma an miƙa shi Sashen Binciken Manyan Laifuffuka don ci-gaba da bincike da kuma ɗaukar matakin shari’a a kansa kamar yadda doka ta tanada.”

Kakakin ya nuna damuwar rundunar na yawaitar aikata laifuffuka irin waɗannan a jihar kasancewar wani mai suna Solomon Asuƙou Isaac ya shiga hannunsu bisa zargin kisan ɗansa mai shekara 18.

Ya ce dukkansu biyu za gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.