✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya harbe abokinsa wajen gwada rigar sulke

A farkon wannan mako ne rana ta baci a lokacin da ake bikin zuwan  sabuwar doya a Assiga da ke Karamar Hukumar Yakurr a Jihar…

A farkon wannan mako ne rana ta baci a lokacin da ake bikin zuwan  sabuwar doya a Assiga da ke Karamar Hukumar Yakurr a Jihar Kurosriba, bayan da wani ya harbe abokinsa da bindiga.

Lamarin ya faru ne lokacin da abokan biyu suka sanya rigunan sulke da aka yi wa maganin bindiga, suka shigo fage ana rawa, ana tsalle-tsalle.

Bisa bayanan da Aminiya ta samu, ya nuna cewa, John Akpama da abokinsa Enang Onun Itam sun sha maganin gargajiya da bindiga ba zata kama su ba, koda kuwa an harbe su. Sannan suka nufo dandalin wasan bikin murnar zuwan sabuwar doya na al’ada da suka saba yi duk shekara.

Daga nan ne sai Onu Itam ya dauko bindiga ya shigo fagen suna rawa da abokin nasa Akpama, shi kuma sai ya ce abokin ya harbe shi, inda ya dirka masa bindigar, kuma a nan take ya fadi matacce, lamarin da ya hargitsa taron. Mutane cikin firgici suka yi ta guda, kafin daga bisani jami’an ‘yan sanda suka zo, suka tafi da gawar zuwa asibiti, inda suke ci gaba da binkice kan lamarin.