✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya harbe kansa a kokarin harbin wani lokacin fashi

Wani mutum da ya harbi wani da bindiga harsashin da ya harba ya dawo ya fasa gilashin motar da yake ciki kuma ya kashe shi.…

Wani mutum da ya harbi wani da bindiga harsashin da ya harba ya dawo ya fasa gilashin motar da yake ciki kuma ya kashe shi.

Mutumin ya ransa ne a cikin mota a yankin Kudu maso Yamma na birnin Landan, bayan da harsashin da ya yi yunkurin harbin wani ya dawo masa, inda ya yi masa mummunan rauni, kuma cikin lokacin kadan ya rasu a lardin Sydenham a yammacin ranar Lahadi, kamar yadda ’yan sandan yankin Scotland Yard suka bayyana.

Wani ganau a yankin ya ce, mutumin ya yi kuskuren kashe kansa ta hanyar harbin bindiga da ya so yi.

“Ya yi kokarin harbin wani sai ya kare da harbin kansa,” inji wata mata mai shekara 56 da ta bukaci a sakaya sunanta.

Matar ta ce, harsashin ya dawo wurin wanda ya harba shi ne ta gilashin kofar motarsa, za a iya ganin shaidar ta inda harshashin ya daka ya dawo, yayin da yaron da mutumin ya yi yunkurin harbi ya zauna gefan hanya yana daukar hoton bidiyon abin da ke faruwa, tunda shi ya tsallake rijiya da baya.

Matar ta ce, ta tsaya cik a kan hanyar da abin ya faru na kimanin awa uku saboda rufe hanyar da ’yan sandan suka yi sakamakon harbin da mutumin ya yi.

Matar wanda ke tsaye a hanyar ta ce, an rufe mutumin da kyalle na kamar sa’o’i uku babu uwa babu uba abin takaici, an dade ba  a samu irin wannan ba. “Na kai kimanin shekara 25 a yankin amma ba a samun irin wannan abu,” inji ta..

Wadansu mutum biyu da suke zaune a kusa hanyar da abin da ya faru sun ji karar harbin bindiga, sun ce sun yi zaton wata mota ce aka harba.

Ba su ji ihu ko wata alamar  inda harbin yake ba, da farko ko bayan an yi harbin.

Wani mutum da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce “Mun ji labarai daban-daban game da abin da ya faru cewa, wani mutum ne a cikin mota da ya yi kuskuren kashe kansa.”

Wani mazaunin shago a hanyar ya ce, yana zaune da shi da abokin aikinsa sai suka ji karar bindiga, daga bisani suka gano cewa, wanda ya yi harbin ne ya kashe kansa.

A cewar rahoton wanda ya yi harbin ya yi fashin motar ce daga hannun masu motar inda ya nuna masu karamar bindiga cewa su fice daga cikin motar, nan take suka fice ya shiga motar, a kokarin da ya yi na harbin wadansu daga cikin wadanda suka mallaki motar sai ya harbe kansa.

Wata mata da ta ga aukuwar abin ta ce, abin ya faru ne a tsakanin hanyar Sydenham zuwa Benner sai ta ji karar bindiga kawai.

”An kai kimanin awa uku kafin ’yan sanda su kammala bincike su a bude hanyar,“ inji ta.

Jami’an ’yan sandan birnin Landan sun ce, a yanzu ba su kama kowa ba, amma suna ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.