✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kai karar Hisba kan daura wa ’yarsa aure a Jigawa

Wani mahaifi ya gurfanar da Hukumar Hisba ta Jihar Jigawa a gaban Kotun Musulunci saboda hukumar ta daura wa wata ’yarsa bazarawa aure da wani…

Wani mahaifi ya gurfanar da Hukumar Hisba ta Jihar Jigawa a gaban Kotun Musulunci saboda hukumar ta daura wa wata ’yarsa bazarawa aure da wani ba tare da sani ko amincewarsa ba.

Hakan ya sa kotun da ke kauyen Sakwaya a ranar Talatar da ta wuce ta aika da takardar gayyata ga hukumar don a saurari yadda al’amarin ya kasance.

Alkalin Kotun Mai shari’a Abdullahi Zandam ne ya aike da takardar sammaci ga Hukumar Hisbar don ta kare kanta game da zargin da mahaifin bazawarar yake yi mata na aura da ’yarsa ba tare da sani ko amincewarsa ba duk da cewa bazawara ce.

Wakilin Hisba kuma shugaban sashen bincike na hukumar  a Jihar Jigawa, Malam Isa Ayuba ne ya wakilce ta a zaman da aka yi a ranar Talatar da ta gabata kuma ya musanta zargin da mahaifin bazawarar Malam Yahaya ya yi na cewar Hisba ta daura wa ’yarsa  Adama aure kai-tsaye.

Ya ce su shaidu ne kawai, ba su suka jagoranci daurin auren ba. Ya ce kanen Malam Yahaya mai suna Malam Mu’azu ne ya daura auren Adama bisa dalilai kamar haka:

Ya ce kanen Malam Yahaya wato Malam Mu’azu ya ce ya yi haka ne saboda gudun kada barna ta auku a tsakanin ’yar. yayan nasa da mai nemanta.  Baya ga haka ya daura mata aure ne a matsayinsa na kanen mahaifinta.

Malam Isa ya kara da cewa dalilin shigowar Hisba cikin batun shi ne Adama ce  ta yi karar mahaifinta Malam Yahaya Sakwaya tana son Hisba ta tursasa mahaifinta a daura mata aure da Mustapha wadda take so, amma lura da cewar Hisba ba kotu ba ce, ta sa suka gayyato dukan bangarorin da suke da ruwa-da-tsaki domin a yi sulhu amma sai mahaifinta wato Malam Yahaya ya ki zuwa sulhun lamarin da ya sa kanensa Malam Mu’azu ya yi amfani da damar ya daura wa Adama aure da Mustapha.

A lokacin da yake yanke hukunci, Mai shari’a Abdullahi Zandam ya ce kotu ta fahimci Hukumar Hisba ba ta da laifi game da wannan aure.  Hasali ma ya dora laifin ne a kan Malam Yahaya game da yadda ya ki yarda Adama ta auri Mustapha duk da suna son juna.  Sannan kotu ta yi la’akari da cewa Malam Mu’azu, kanen Malam Yahaya yana da damar daura wa Adama aure a matsayinsa na kanen mahaifi.

Sai dai kotu ta lallashi Malam Yahaya ya amince da auren da aka daura a tsakanin Adama da Mustapha duk da rokon da Malam Yahaya ya yi na kotu ta bata auren.

Sannan kotu ta gargadi Hukumar Hisba da ta rika yin taka-tsantsan game da shiga irin wannan rikici ba tare da ta yi kwakkwaran bincike ba da hakan ka iya kawo rudani.

Jim kadan da kammala zaman kotun alamu sun nuna Malam Yahaya, mahaifin Adama ya amince da auren da aka daura wa Adama tare da angonta Mustapha.