Da Dumi Dumi

Ya kamata gwamnati ta soke bara da almajiranci – Babban Limamin Dutse 

Almajirai a layin

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Dutse kuma Babban Sakatare a Hukumar Makarantun Arabiyya da Harkokin Addini ta Jihar Jigawa, Malam Abubakar Sami Birnin Kudu ya bukaci gwamnati ta hana bara da almajiranci domin suna cikin matsalolin da suka addabi Arewa.

Limamin ya ce almajiranci kaskanci ne ba na neman ilimi ba ne, inda ya ce, wadansu iyaye sun haifi ’ya’ya ba sa iya ba su kular da ta dace, sai su rika tura yara kanana almajiranci sai sun yi bara su ci da kansu.

Malam Abubakar ya kara da cewa mafiya yawan yaran da ke yin almajiranci sai su shafe shekara hudu suna yawo a kauyuka da birane ba su da tilawar izifi biyu, amma yara kanana a gaban iyayensu wadanda suke samun kulawa kan karatun addini suna da tilawar izifi 40.

Ya ce lalacewar karatun allo laifin iyayen yaran ne da suke hada ’ya’yansu da malami a kai su makaranta don kawai iyaye su yakice su daga jikinsu saboda ba za su iya yi musu duk abin da ya kamata na kula ba.

Ya bada shawarar cewa Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohin Arewa su soke almajiranci saboda ana, “tozarta mu kuma barin almajiranci ya ci gaba da yiwuwa yana ba wa wadansu iyayen damar wulakanta ’ya’yansu,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Malamin ya ce zai yi wahala ’yan siyasa su amince da shawarar saboda suna kwadayin kuri’a lokacin zabe, “duk wanda ya ce ya soke almajiranci da bara a jiharsa ko a karamar hukumarsa  wadansu za su yake shi a lokacin zabe,” inji shi.

 

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya