✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata Hukumar Hajji ta sake tsarin kiwon lafiya – Muntari Lawal

Amirul Hajji na bana na Jihar Katsina Alhaji Muntari Lawal ya yi kira ga Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON) ta sake duba tsarinta na malaman…

Amirul Hajji na bana na Jihar Katsina Alhaji Muntari Lawal ya yi kira ga Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON) ta sake duba tsarinta na malaman kiwon lafiya a lokacin aikin Hajji.

Amirul Hajjin wanda kuma Babban Sakatare ne a Ofishin Gwamnan Jihar ya yi kiran ne lokacin da yake yi wa wakilin Aminiya bayani bayan kammala dauko alhazan jihar, inda ya ce “Wani alhajin har a gama aikin Hajjin bai iya gano inda asibitin da NAHCON ta kebe balle ya je in yana da wata lalura. Ni kaina akwai lokacin da na samu wani mara lafiya na kira likita na ce ga wani ba ya da lafiya, sai ya ce mini to shi me zai iya yi, domin babu magani a hannunsa. Ka ga wannan ba karamar matsala ba ce,” inji shi.

Alhaji Muntari Lawal ya bukaci Hukumar NAHCON ta ba kowace jiha dama ta tafi da likitocinta da magunguna da sauran ma’aikatan lafiyarta, sannan ta samar da wajen kula da marasa lafiya a can Kasa Mai tsarki a lokacin aikin Hajji. “Amma tsayar da kiwon lafiya waje daya a kasa baki daya ba karamin aiki ba ne kuma hakan zai ci gaba da bayar da matsala musamman ga marasa lafiya domin kafin su gano inda za su je za su iya shiga cikin wani hali,” inji shi.

Da ya juya kan yadda aikin Hajjin bana ya gudana, Amirul Hajjin ya jinjina wa alhazan Jihar Katsina kan yadda suka tsare dokokin da aka ce su tsare.

Ya ce, “Babu abin da za mu ce wa Gwamna Aminu Masari sai dai addu’a. Hakan ne ya sa mahajjatan bana suka yi wa jihar da kasa Dawafi na musamman tare da yin addu’o’in samun zaman lafiya kan hare-haren da ake samu a jihar da kasar nan.”

Alhaji Muntari Lawal ya kuma jinjina wa Alhaji Dahiru Mangal mai jiragen Mad Air wanda ya kwashe shekara 10 yana daukar alhazan Jihar Katsina.