✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata jama’a su rika saye da sanya talla a Aminiya – Dagacin Jabi

An yi kira ga daukacin al’ummar garin Abuja da su ci gaba da saye tare da sanya talla a cikin jaridar Aminiya don bunkasa cinikin…

An yi kira ga daukacin al’ummar garin Abuja da su ci gaba da saye tare da sanya talla a cikin jaridar Aminiya don bunkasa cinikin jaridar a birnin tarayya.

Dagacin yankin Jabi, Alhaji Yakubu Auta shi ne ya yi kiran a yayin da Mataimakin Manajan Kasuwanci na Jaridar Aminiya ya kai masa ziyara a fadarsa da ke yankin Jabi a ci gaba da bunkasa cinikin jaridar a ranar Juma’ar da ta gabata, a Abuja.

“Aminiya jarida ce mai tsage gaskiya wacce ba ta yin karin gishiri a labaranta. Saboda haka nake kira ga daukacin al’ummar garin Jabi da Abuja baki daya su ci gaba da sayen jaridar tare da sanya tallace-tallace a cikinta don bunkasa cinikin jaridar”. Inji shi.

Auta wanda har ila yau shi ke rike da sarautar Etsu Jabi ya yaba wa hukumar gudanarwar kamfanin Aminiya dongane da zabar yankin Jabi domin gudanar da kalankuwar bunkasa cinikin jaridar.

Da yake jawabi a fadarsa, Sarkin Hausawan Jabi, Alhaji Aliyu Abubakar ya bayyana jaridar Aminiya a matsayin jaridar da ke ilimintarwa tare da wayar da kan al’umma.

Ya yi kira ga daukacin Hausawan yankin Jabi su rika sayen jaridar don samun fa’idar rayuwa. Haka shi ma Babban Limamin Masallacin Juma’a na Jabi, Shaikh Yakubu Ahmad ya yaba wa tawagar Mataimakin Manajan Kasuwancin na Aminiya da kuma shugabannin kamfanin jaridar saboda namijin kokarin da suke yi na bunkasa cinikin jaridar a kodayaushe.