Da Dumi Dumi

Ya kamata  jihohi su yi koyi da Zamfara kan dokar hana tsofaffin gwamnoni fansho

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’azez Yari Abubakar ya kasance Gwamnan da ya rika zama abin kallo da magana a tsakannin mutanen jiharsa da na kasa baki daya da ma tsakanin  takwarorisa na jihohi lokacin da yake ofis da bayan ya bar ofis a watan Mayun bana.

A lokacin da tsohon Gwamna Yari yake mulki, musamman a zangonsa na karshe 2011 zuwa 2015, hare-haren ’yan bindiga da sace-sacen shanu da uwa uba masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa da sauran miyagun ayyukan ta’addanci suka yi kamari a sassan jihar, maharan sun hana tafiye-tafiye walau don zumunci ko cin kasuwanni ko sauran hidimomin yau da kullum a jihar da wajenta.

A wancan lokaci duk da irin mawuyacin halin rashin tsaron da Jihar Zamfara ke ciki, kusan a kullum Yari ba ya zama a jihar, ko dai yana Abuja ko yana kasashen waje, tafiye-tafiyen da za a iya cewa ba su tsinana wa mutanen jihar komai ba, duk da  cewa da kudinsu ake yin su. Har sai da ta kai ga fagen da wani Sarkin yanka a jihar ya fada wa Gwamnan cewa lallai ya rika zama a jihar don magance mummunar annobar da ta addabe ta. Haka takwarorinsa gwamnonin jihohi, amma duk lokacin da aka ba tsohon Gwamna Yari irin wadancan shawarwari,  za ka tarar yana da hanzarin da zai bayar.

Take-taken tsohon Gwamna Yari wanda kuma ya rike mukamin Shugaban Kungiyar Gwamnonin  Kasar nan, na sai yadda yake so za a yi (kamar yadda sauran takwarorinsa na jihohi suka saba yi) ta kai jam’iyyarsu ta APC rasa mulkin jihar tun daga kan mukamin Gwamna da na ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa da na jihar baki daya ga jam’iyyar adawa ta PDP, wanda shi ne karon farko da haka ta taba faruwa tunda aka fara mulkin dimokuradiyya yau shekara 20, ba a Jihar Zamfara ba a kasa baki daya.

Haka ya faru a kan irin yadda tsohon Gwamna Yari ya tsaya kai-da-fata a kan shi kadai zai tsayar (ko nada) wadanda za su tsaya wa jam’iyyarsu ta APC takara a wadancan mukamai a jihar.

ADVERTISEMENT

Al’amarin da ya janyo bayan shigar da kara da ’ya’yan Jam’iyyar APC suka yi na kalubalantar yadda aka yi zaben fitar-da- ’yan takarar, Kotun Koli ta yanke hukuncin  cewa Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara ba ta da ’yan takara a zaben bana, saboda dukkan ’yan takararta ba ta fitar da su a kan ka’idoji  da sharuddan da uwar jam’iyyar ta kasa ta shimfida ba, don haka kotun ta yanke hukuncin  ’yan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, su suka ci zaben tun daga sama har kasa!

Ko shakka babu kama-karya da nuna isa ta tsohon Gwamna Yari ita ta kai Jam’iyyar APC da shi kansa rasa jihar baki daya (don shi ma ya ci takarar Sanata a wancan lokaci).

Saukarsa ke da wuya sai kuma Hukumar EFCC ta rufe asusun ajiyarsa da ke dauke da miliyoyin Naira bisa zargin kudaden haram ne. Duk da irin kokarin da tsohon Gwamna Yari ya yi don ganin kotu ta cece shi don maido masa da kudinsa,  al’amarin ya ci tura.

Ana cikin haka sai ’yan bindiga suka kai hari a kauyen Karaye a  jihar  inda suka kashe mutane da dama a daidai lokacin da sabuwar gwamnatin jihar take kokarin kawo karshen ta’addanci a jihar. Harin ya zo ne a daidai lokacin da tsohon Gwamna Yari ya ziyarci jihar.  Gwamna Matawalle ya zargi tsohon Gwamnan da cewa shi ne kanwa uwar gami cikin tashin rikicin. Zargin da tsohon Gwamna  Yari ya musanta.

Ana cikin wancan sa-in-sa kuma sai tsohon Gwamna Yari ya rubuta wa Gwamna Matawalle wasika da aka tona asirinta, yana neman gwamnatin jihar ta biya shi Naira miliyan goma na kula da shi da kudinsa na fensho wanda yake daidai da albashin Gwamna. Dukkan kudaden na wata-wata ne da tsohon Gwamna Yari ya ce bayan ya sauka an biya shi (kudin kula da kansa) na watan Yuni da Yulin bana. Tsohon Gwamna Yari dai, shi ya sa Majalisar Dokokin Jihar ta gyara waccan doka da ta tanadi bayin kudin sallama da na fansho ga wasu tsofaffin shugabannin farar hula na Jihar Zamfara da suka hada da Gwamna da Mataimakinsa da kuma Shugaban Majalisar Dokokin Jihar da Mataimakinsa, ya kuma sa hannu a ranar 23 ga Maris din bana.

Tsohon Gwamna Yari yana jiran a ci gaba da biyansa wadancan kudade da ya ce hakkokinsa ne sai ga shi a makon jiya Majalisar Dokokin Jihar ta yi gyara a kan daftarin waccan doka, inda ta soke biyan wadancan kudade ga wadancan shugabanni a jihar.

Da yake sa hannu a kan dokar an ruwaito Gwamnan Jihar Alhaji Bello Matawalle, yana cewa sun dauki wannan mataki ne bayan da ya kira taro da Mataimakinsa da kuma Shugaban Majalisar Dokoki da Mataimakinsa, inda ya tambaye su ko suna da bukatar amfana daga waccan doka a nan gaba, amma suka ce ba su da bukata.

Gwamna Matawalle ya ce yanzu gwamnati za ta rika samun Naira miliyan 702 duk shekara daga daina biyan wadancan kudade. Dadin-dadawa ya ce duk wanda ya kai ga rike mukami irin nasu ba matalauci ba ne kafin ya zo kan kujerar. Ya kuma zargi tsohon Gwamna Yari da dibar Naira miliyan 360 daga asusun fansho na jihar, wadanda ya biya kansa kudin sallama. Ya kuma zargi tsohon Gwamna Yari da kin biyan ’yan fansho hakkokinsu na tsawon shekara shida daga cikin takwas da ya kwashe yana mulkin jihar.

Tun a shekarar 2007, gwamnonin jihohi suka rika sa majalisun dokokin jihohinsu suna tanadar dokokin da za su rika biyansu kudade da alawus-alawus na sauka daga mukamansu.

Wasu daga cikin kudade da alawus-alawus da dokokin suka tanada, bayan biyansu miliyoyin Naira a matsayin kudaden sallama da na kula da kai da na fanshon wata-wata, sauran sun hada da saya wa tsofaffin gwamnonin gidajen alfarma a jihohinsu da Abuja (bisa ga yadda dokar kowace jiha ta tanada). Akwai kuma alawus-alawus na kayayyakin kawata gida da motocin alfarma da na kiwon lafiya da makamantansu.

Ina ganin bisa ga irin yadda gwamnatoci, musamman na jihohi suke fama da matsalolin rashin kudin shiga da za su rika tafiyar da ayyukan raya kasa irin na ilimi  da kiwon lafiya da samar da ruwan sha da makamantansu, ya kamata sauran jihohi su daure su yi koyi da Majalisar Dokokin Jihar Zamfara wajen soke waccan doka. Na yarda da abin da Gwamnan Jihar Zamfara ya fadi cewa duk wanda ya samu zama Gwamna ko Mataimakinsa ko Shugaban Majalisa ko Mataimakinsa ba fakiri ba ne kafin zuwansa wannan mukami.

Share