Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Ya kamata masu yabon Manzon Allah su rika koyi da shi – Tagwayen Ma’aiki

Hassana da Hussaina Abubakar

Hassana da Husaina Abubakar wadanda aka fi sani da Tagwayen Ma’aiki, mawakan yabon Annabi (SAW) ne a Kano. A tautawarsu da Aminiya sun yi kira ga sha’irai su zama masu koyi da halayen Manzon Allah:

 

ADVERTISEMENT

Za mu so sanin tarihin rayuwarku.

Sunanmu Hasana da Hussaina Abubakar. An haifemu a Unguwar Gwale Filin Mushe,  Kano. Mun yi karatun firamare a makarantar firamare ta Sani Mainagge. Mun yi karamar sakandare a Makarantar Adamu Nama’aji sannan muka yi Babbar Sakandiren Arabiyya da ke Gwauron Dutse. Bayan mun kammala sai muka tafi Makarantar Koyon Harkokin Shari’a ta Malam Aminu wacce aka fi sani da Legal inda muka samu shaidar difloma. To tun daga nan kuma ba mu ci gaba da karatu ba sai muka yi aure.  A yanzu Hassana tana zaune a Unguwar Sabon Titi, Hussaina kuma tana zaune a Unguwar Dorayi.

ADVERTISEMENT

Yaya aka yi kuka fara wakar yabon Ananbi (SAW)?

Za mu iya cewa tun muna kanana muka fara wato daga irin kasidun da ake ba mu a makaramntun Islamiyya muna yi a wajen Maulidi. Daga baya kuma sai muka fara rubutawa da kanmu. Sai kuma ga shi Allah Ya sa muka ci gaba har zuwa wannan lokaci inda har a kan gayyace mu majalisi ko wuraren maulidi ko wurin suna ko bikin aure da sauransu.

Yaya aka yi ra’ayinku ku biyun ya zo daya a wannan harka?

To za mu iya cewa tun muna kanana a’ayinmu ya zo daya. Hakan ya ba mu damar ci gaba har zuwa wannan lokaci. A yanzu haka duk da ba unguwa daya muke zaune ba amma a kullum muna tare, domin tare muke tafiya wajen majalisi ko kuma idan an gayyace mu maulidi da sauran bukukuwa.

Yaya kuke hada kasidunku?

Idan misali daya a cikinmu ta rubuta kasida to za ta kawo wa dayar don ta duba ta kara nata baitocin a kai. Sannan mu hadu mu yi mata gyare-gyare mu kuma fitar mata da karin da muke ganin zai dace da ita. Sai mu mika ta ga na gaba da mu a fagen domin su yi mana gyara. Daga baya kuma sai mu kai sutudiyo a buga mana.

Kasancewarku matan aure ba ku samu wani kushe a kan abin da kuke yi ba?

A gaskiya ba mu samu ba domin tun kafin mu yi aure muke yin wannan abu. Kowa ya sani har mazanmu a ciki suka aure mu. Idan ma za a ce ko ana yin surutu kana lamarin to sai dai ko ta bayan fage. Kullum idan mutum yana cikin lamarin Manzon Allah (SAW) abin da yake dubawa shi ne nasara shi ya sa mutum ma ba zai tsaya duba wasu kalubale da ke gabansa ba.

Ana zargin masu yabon Annabi da yi wa juna hassada me za ku ce a kan hakan?

A gaskiya akan samu wadansu daga cikinmu da irin wannan hali. Wani za ka ga tsohon sha’iri ne amma idan wani ya zo daga baya ya fi shi daukaka sai ya rika yi masa hassada wannan abu bai dace ba. Mu dai a gaskiya muna da kyakkyawar mu’amala da sauran sha’irai. Muna girmama juna. Ko yanzu kika nemi mu kawo miki sha’irai tun daga manya har kanana za mu kira miki su, domin akwai alaka kyakkyawa a tsakaninmu.

Wane kira kuke da shi ga sauran ’yan uwanku sha’irai?

Yana da kyau duk wani sha’iri idan ya rubuta kasidarsa to ya kai ta wurin malamai ko shugabanninmu na kungiyoyinmu na sha’irai su duba masa, saboda kada ya je ya gaya wa Annabi (SAW) wata kalma da ba ta dace ba. Akwai bukatar sha’irai su nemi ilimi ko su kara zurfaf iliminsu domin tafiyar da ba ilimi a ciki ba ta dorewa. Ya kamata kafin ka yi wa Shugaba (SAW) yabo ka san shi ka san dabi’unsa da halayensa da siffofinsa, Hakan ne zai ba ka damar yin yabo tsarkakke.

Har ila yau akwai bukatar masu yabon Manzon Allah su kasance masu koyi da dabi’unsa da kuma halayensa. Kana cewa kai mai son Manzon Allah ne ga shi kana kasida amma idan an dube ka babu dabi’ar Manzon Allah a tare da kai. Idan an je unguwarku makwabtanka ba za su bayar da shaida mai kyau a kanka ba. Idan har aka same ka ba ka da kyakkyawar mu’amala tsakaninka da mutane to Annabi (SAW)  ma babu ruwansa da kai.  Mu tuna fa kaunar Annabi ita ce ka bi umarninsa ka kuma guji abin da ya yi hani a kansa.