✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata mulki ya koma kudu a 2023 – El-Rufa’i

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ya ce kamata ya yi mulki ya koma yankin Kudanci idan Shugaba Buhari ya kammala wa’adinsa a 2023. A hira…

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ya ce kamata ya yi mulki ya koma yankin Kudanci idan Shugaba Buhari ya kammala wa’adinsa a 2023.

A hira da ya yi da Sashen Hausa na BBC, El-Rufai ya ce duk da dai ba a rubuce tsarin na karba-karbar da ake amfani da shi a siyasance yake ba, yana da kyau a mutunta shi tun da kowane bangare ya yi na’am da shi.

“Akwai tsarin da ake bi na karba-karba, inda kowa ya amince cewa idan Arewa ta yi mulki shekara takwas, Kudu zai yi mulki shekara takwas”, inji El-Rufai.

Ya kara da cewa, “Shi ya sa na fito na ce bayan Shugaba Buhari ya yi shekara takwas, kada wani dan Arewa ya nemi mukamin. A bar ‘yan kudu suma su samu shekara takwas”.

To sai dai sabanin yadda ake ta hasashe, gwamnan ya ce sam ba shi da sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Ya ce, “Allah Shi Yake ba da mulki, ko kana so ko ba ka so idan yana so zai ba ka amma ni ban taba neman shugabancin Najeriya ba, ba wanda zai ce na taba nema,” inji gwamnan.

An dade ana harsashen yiwuwar tsayawarsa takarar idan Buhari ya kammala wa’adinsa, yayin da wasu kuma suke kira da cewa lokaci ya yi da kasar za ta yi watsi da tsarin na karba-karba ta koma zaben cancanta.

Ko a kwanakin nan, kiran da wani makusancin Shugaba Buhari, Mamman Daura ya yi cewa lokaci ya yi na jingine yanki a bi cancanta wajen zaben magajin Buharin a 2023 ya tayar da kura.