✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kashe dansa saboda ya cinye masa faten doya

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kuros Riba ta kama wani mai suna Okon Emmanuel, bisa zarginsa da kashe  dansa saboda ya shanye faten doyar da aka…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kuros Riba ta kama wani mai suna Okon Emmanuel, bisa zarginsa da kashe  dansa saboda ya shanye faten doyar da aka dafa musu za su ci tare. Wata ’yar sanda mai suna Etebong ta shaida wa manema labarai haka lokacin da take gabatar da wanda ake zargi da sauran wadanda ake zargi  kan laifuffuka daban-daban ga manema labarai a madadin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Mista Austin Agbonlahor, inda Kakakin Rundunar Irene Ugbo ta ce an kama su ne a wurare daban-daban na jihar.

Ana zargin Okon ya kashe dansa ne a Karamar Hukumar Akamkpa ta Jihar Kuros Riba.

Kuma daga  cikin wadanda aka kama bisa zargi har da wani shahararren mai kama mutane ana yin garkuwa da su domin karbar kudin fansa da ’yan sanda suka dade suna nemansa ruwa a jallo mai suna Micheal Etim wanda ake yi wa lakabi da Aso Rock.

Shi kuma asirinsa ya tonu ne a wani samame da sashen masu yaki da ’yan fashi da sauran ayyukan ta’addanci ya kai yankin Bakassi .

Aminiya ta tambayi Okon Emmanuel, da ake zargi da kashe dansa saboda ya cinye abincinsu, sai ya ce, “Abinci ne aka dafa mana faten doya aka zuba mana, sai na tafi in debo mana ruwan sha kafin in je in dawo ya cinye abincin ko da na tambaye shi ina abincin yake don mu ci sai ya kada baki ya ce da ni baba na cinye abincin duka ni kadai,” inji shi.

Ya ce jin wannan amsa daga dansa “Maimakon in yi hakuri sai raina ya baci na dauko wata sanda na fara dukansa da ita ya gudu na bi shi na dauki wata katuwar sanda na buga masa a kai ya fadi sumamme abu kamar wasa aka kwashe shi kafin a yi wani kokari na tafiya asibiti har rai ya yi halinsa shi ne ’yan sanda suka zo suka kama ni,” in ji shi.

Sauran ragowar mutum 26 da rundunar ’yan sandan ta kama, ana zarginsu da aikata fyade da zama ’ya’yan kungiyar asiri da fashi da makami da garkuwa da mutane don karbar kudin fansa da sauransu.

Bayan Kakakin Rundunar ta kammala nuna wa ’yan jarida wadanda aka kama, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kuros Riba Austin Agbonlahor ya ce “Kokarin jami’anmu tare da hadin kan jama’ar gari ne ya sa muka samu nasarar wannan kame, kuma da zarar mun gama bincike za a mika su kotu domin yi musu hukunci da ya dace.”