✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kashe matarsa kan zargin yin lalata da maza

Wani mai suna Ihenacho Nkem ya kashe matarsa  mai suna Regina da duka a lokacin da suke fada kan zargin tana yin lalata da maza.Mista…

Wani mai suna Ihenacho Nkem ya kashe matarsa  mai suna Regina da duka a lokacin da suke fada kan zargin tana yin lalata da maza.
Mista Ihenacho Nkem, dan kimanin shekaru 34, wanda dan uwan tsohon Ministan cikin gida, Kyaftin Emmanuel Ihenacho (mai ritaya) ne, ya kama matarsa mai suna Ragina, ’yar kimanin shekaru 30 da kokawa inda ya rika naushin ta har sai da fadi kasa matacciya saboda ta yi lattin dawowa gida.
Lamarin ya faru ne a cikin watan da ya gabata da misalin karfe 12 na dare a gida mai lamba 3 da ke layin Calbary a unguwar Mebano Shashi a Jihar Legas.
Wani makwabcinsu, wanda bai so a bayyana sunansa ba, ya shaida wa Aminiya cewa Ihenacho sun dade suna yin rikici kan zargin da mijinta yake yi mata na yin lalata da maza a waje.
Majiyar ta ce kullum sai sun yi rigima, musamman idan ta yi lattin dawowa daga kasuwa inda take sayar da kayan masarufi.
Majiyar ta ce, “Lokacin da ya dake ta ta fadi warwas, mun yi kokarin kai ta asibiti, amma muna zuwa sai likitoci suka ce ta mutu.
Makwabtansu sun bayyana Regina a matsayin mace mai hakuri, mai juriya tare da neman na kanta.
Shi kuwa Nkem sun bayyana shi a matsayin wanda ba shi da hakuri sannan kuma mutum ne wanda ba shi da yarda.
Aminiya ta gano cewa Ihenacho ya yi kokarin kashe maganar, amma makwabtansa suka ki yarda inda daga bisani suka kai kara wurin ’yan sanda.
Daga bisani an kama shi an kai shi sashen bincike na ’yan sanda da ke unguwar Yaba, inda bayan nan aka gurfanar da shi a kotun gargajiya da ke unguwar Ebute Meta.
Alkalin kotun, Mista O. O. Olatunji ya ba da umarnin daure shi a gidan maza, sannan kuma ya ba da umarnin a kai fayil dinsa hukumar ba da shawara kan manyan laifuka.
Bayan kwanaki sai aka sake komawa katu, inda alkalin ya ba da belinsa kan Naira dubu 200 tare da shaidu biyu, wadanda aka bukaci kowanensu ya mallaki Naira dubu 200, sannan ya sake dage ci gaba da shari’ar zuwa karshen wata.