Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Dalung ya nemi majalisa ta ware wa  harkar wasanni kaso mai tsoka a kasafin kudin bana

Barista Solomon Dalung, Ministan Matasa da Wasanni

Ministan Matasa da Wasanni Barista Solomon Dalung ya nemi Majalisar Dokoki ta Kasa  ta yi wa Allah ta ware wa bangaren wasanni kaso mai tsoka a kasafin kudin bana.

Barista Solomon Dalung ya bayyana haka ne lokacin da yake taya ’yan wasan kokuwa bangaren mata na Najeriya murnar lashe Gasar Kokuwa ta Afirka da aka kammala a kasar Tunisiya inda Najeriya ta zama zakara.

ADVERTISEMENT

Najeriya ta lashe gasar ce bayan ta lashe lambobin zinare 6 da azurfa 2 da kuma tagulla 6.  Da ma Najeriya ce zakara a gasar da aka yi a baya, don haka yanzu ta sake rike kambunta.

A karshen gasar ce aka zabi Najeriya a matsayin wacce ta fi yin kwazo a bangaren kokawa ta mata a Afirka.

ADVERTISEMENT

Ganin wannan nasara da kungiyar ta samu ne ya sa Minista Dalung ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya kan ta ware wa harkar wasanni kaso mai tsoka da kasafin kudin bana.

Barista Dalung ya ce “Ko nawa gwamnati ta kashe a bangaren wasanni ba za ta fadi ba, don harka ce mai janyo wa kasar nan daukaka da martaba a idon duniya da hakan zai janyo masu zuba jari da yawa zuwa cikn kasar nan.

Haka kuma Barista Dalung ya nemi gwamnati ta daina fifita harkar kwallon kafa a kan sauran wasanni, inda ya ce hakan yake kawo koma-baya a wasu wasannin.

“Ba harkar kwallo ce kadai harkar wasa ba, ya kamata a rika mutunta wasu wasanni kamar yadda kasashen da suka ci gaba suke yi,” inji Dalung.