Da Dumi Dumi

Ya yanka surukarsa, ya kuma sha guba ya mutu

Wani magidanci mai suna Boke, mai kimanin shekara 44 ya yi wa surikarsa yankan rago ya sha jininta. Surukar wadda ba a baiyana sunanta ba, lamarin ya faru ne a yankin Arubayi a Karamar Hukumar Warri ta Kudu a Jihar Delta.

Samun labarin kisan kai ke da wuya sai matasan unguwar suka yi gangamin don daukar wa matar fansa sai aka iske ya mutu.

Bayanin da wakilin Aminiya ya samu ya nuna ana tsakiyar cin kasuwa da ke Mararrabar Polokor, sai labari ya bazu  cewaBoke ya kashe surukarsa, kuma koda matasan unguwa  suka isa wurin da ya kashe surukar tasa sai suka iske gawarsa a kusa da gadar Polokor inda ya kashe surukar.

Jami’an ’yan sanda na Shiyya ta “B” sun garzaya wurin da abin ya faru kuma sun iske gawar mutum biyu, Boke da ta surukarsa inda suka kwasshe su zuwa ofishinsu da ke Warri. An gano wanda ake zargin ya kwankwadi guba ce bayan ya yi kisan kan wadda ta yi ajalinsa. Bayanan da wakilinmu ya samu sun ce Boke yana da ’ya’ya biyar da ’yar surukarsa da ya kashe mai suna Onome.

Wata majiya da ke kusa da iyalan mamaciyar da ta bukaci a sakaya sunanta ta shaida wa Aminiya cewa, “Tun farko sai da faston majami’arsu ya gargade ta cewa, kada ta kuskura ta ba Boke auren ’yarta, domin so yake ya yi tsafi da ’yarta duk da cewa, bai biyan kudin auren ’yarta na al’ada ba.”

ADVERTISEMENT
Share