✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya yi daidai malaman addini su rika sanya baki a harkokin siyasa?

A daidai lokacin da zabubbukan badi suke kara karatowa, yakin neman zabe na kara zafi, inda musamman yanayin kamfe ke kara canja salo. A lokuta…

A daidai lokacin da zabubbukan badi suke kara karatowa, yakin neman zabe na kara zafi, inda musamman yanayin kamfe ke kara canja salo. A lokuta da dama, idan malamai suka yi magana a kan siyasa, mutane musamman wadanda aka taba bangaren da suke so sukan yi maganganu marasa dadi a kan malaman. Wannan ne ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane a kan wannan maudu’i kuma ga abin da suke cewa:

 

Bai dace ba – Sirajo Aliyu Sujee

Daga Nasiru Bello, Sakkwato

Sirajo Aliyu Sujee: “Bai dace su rika sanya baki ba. Idan wadansu na da ra’ayin batanci gare su da zarar sun yi magana sai a shafa musu kashin kaji ana yi musu yarfe da iyalansu da addini da almajiransa. Don haka su cire ko su nesanta kansu da siyasa don rike kima da mutuncinsu da addini. Don haka bai dace su rika sanya kansu a siyasa ba.”

 

Bai kamata ba a ra’ayina – Misis Mary Enwongulu

Daga John D. Wada, Lafiya

Mary Ewongulu: “Ni dai a ra’ayina bai kamata malamanmu na addini su rika sa baki a harkokin siyasa ba. Idan ya zama dole su sa baki, to a matsayinsu na shugabanninmu na addinai ya kamata ne su rika ba da shawarwari da gargadi ga ’yan siyasa da sauran al’umma baki daya game da bukatar a rika yin siyasar cikin kwanciyar hankali da tsoron Allah. Ba wai su rika shiga siyasar dumu-dumu ana yi da su ba. A ganina hakan bai cancanta ba.”

 

Wajibi ne a kan malamai – Usman Umar

Daga Adam Umar, Abuja

Usman Umar: “Ai wajibi ne ma. Illa dai mun samu kanmu a cikin wani yanayi a kasar nan na ita kanta siyasar ta shiga kowane bangare na jama’a ta gurbata su. Malamai a saninmu su ne jagorori a dukan bangarorin al’umma kuma ko da kasashen da ke tinkahon ci gaba a siyasa irin su Amurka ai ka ga taken kasar shi ne “Da Allah muka dogara,” duk da akidar kasar ta cewa kowa na da ’yancin yin abin da yake so. Sai dai shigarsu a harkar za ta kasance ce ta fuskar fadakarwa ciki har da su kansu ’yan takara ta hanyar hikima, duk da cewa akwai yanayi da zai sa a kai ga kebewar amma ya zamana ga wanda aka gamsu da adalcinsa ba wanda ake masa ganin akasin haka ba.”

 

Wajibi ne su rika sanya bakinsu amma–Murtala Da’a

Daga Nasiru Bello, Sakkwato

Malam Murtala Da’a: “Wajibi ne malamai su rika sanya bakinsu a harkokin siyasa. Kamar yadda aka sani kalmar siyasa Larabci ce da ke nufin shugabanci, raba siyasa da addini sabon abu ne da ba a san da shi ba. A ka’ida ta Musulunci shugabanci biyu ne malamai da jagorori, malamai su ne masu ruwa da komai su shiga harkar kasuwanci da tarbiyya da shugabanci da sauran lamuran siyasa. Abin da kawai nake gani kuskure ne su alakanta kansu da wata jam’iyar siyasa ko batanci da aibantawa ga wasu da soke-soke na banza amma in ka yi magana kan abin da addini ya ce ga wanda ya kamata a zaba ko a bar shi, wasu suka fassara ka ai wane ko jam’iya ka za kake yi to ba ruwanka su ne ke da hakki. Ina kira ga masu raba addini da siyasa su bari komai za ka yi a ruyuwarka akwai matsayar addini a ciki ko ka sani ko ba ka sani ba don haka kuwa wadanda suka san addinin wajibi ne kansu su fadi matsayar addini kan duk wani lamari da za a yi.”

 

A gaskiya bai dace ba –Hussaini Abdullahi

Daga John D. Wada, Lafiya

Hussaini Abdullahi: “A gaskiya bai dace malaman addinanmu suna shiga siyasa ba. Don hakan zai iya zubar musu da mutunci da martaba ya kuma jawo musu bakin jini daga wajen mabiyansu don wadansu za su rika zarginsu cewa suna goyon bayan bangare daya. Saboda haka a takaice ra’ayina shi ne bai dace shugabanni ko malamanmu na addini su shiga harkar siyasa ba. Ko kadan bai dace da su ba.”

 

Sun fi cancanta su sanya baki  sai dai – Bello Buba Gombe

-Daga Adam Umar, Abuja

Bello Buba Gombe: “Sun fi kowa cancantar shiga hakar saboda su ne fitila da ke haskakawa ga al’umma. Idan sun fada mutane za su fi daukar lamarin da muhimmanci fiye da shi kansa dan siyasar. Sai dai kamata ya yi su yi amfani da hannunka mai sanda wajen fadakarwar tare da jan hankali ta hanyar lalama. Ba daidai ba ne malami ya nuna inda ya karkata karara, idan haka ta faru to lallai zai jawo rabuwar kai a tsakanin al’umma sannan kimarsa ta zube, saboda za a fara zargin kudi ne aka ba shi ko kuma akwai shigowar wani abu na rashin gaskiya.”