✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda a ka kashe wani darakta kwana 2 gabanin kara masa girma

Iyalan wani mataimakin darakta da ke aiki a sashen ba da ayyukan kwangila wato (Department of Procurement Unit) a Ma’aikatar kula da Birnin Tarayya Abuja…

Iyalan wani mataimakin darakta da ke aiki a sashen ba da ayyukan kwangila wato (Department of Procurement Unit) a Ma’aikatar kula da Birnin Tarayya Abuja (FCTA), suna ci gaba da juyayin yadda a ka yi wa mamacin kisan gilla kwana biyu gabanin yi masa karin girma zuwa matsayin mukaddashin darakta.
Malam Abdullahi dahiru dai ya gamu da ajalinsa ne kwana guda bayan dawowarsa Abuja daga garinsu (Keffi) da ke jihar Nassarawa inda ya je bikin karamar Sallah, inda da daddare wasu wadanda ba a shaida ba suka kutsa cikin gidansa da ke unguwar GRA Keffi, kuma suka kashe shi.
Da yake bayyana wa Aminiya yadda al’amarin ya faru, wani dan uwan marigayin, mai suna Yahaya Rajab, ya ce, a ranar Talata 29 ga watan jiya, ya rabu da dan uwan nasa a gidansu na iyaye da ke kusa da fadan sarki a Keffi da misalin karfe 6:00 na marece, inda marigayin ya umarce shi da ya je wani banki da ke Mararaba kusa da Abuja washegari Laraba don karbo masa kudi, amma bayan dawowarsa ya nufi gidan nasa don kai sakon, inda ya jima ya na buga kofar gidan daga waje ba tare da an amsa masa ba.
“Na nemi layukan wayarsa biyu ba tare da sun shiga daga nan ne na dawo gidana kasancewar na san shi kadai ne a gidan saboda amaryarsa da su ka taho sallah tare ta riga ta wuce Abuja. Daga bisani ne bayan na koma gidansa, wani kanina ya bayyana min cewa ya ga motarsa da misalin karfe 10:00 na dare da yana tukata cikin gudu da rashin natsuwa. Daga nan ne na fara shiga damuwa, inda muka yanke shawarar sake dawowa gidan. Da isar mu sai muka tadda kofar gidan a bude,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa yanayin da suka samu gawar marigayin kwance a kasa a cikin turakarsa ya sa shi yanke jiki ya fadi, sannan dan uwan nasa ya ruga waje cikin dimuwa yana kuka. Ya ce “mun samu kafafunsa da hannayensa an dauresu, sai wata igiyar da a ka daurata a tsakanin labbansa biyu a ka daurota ta bayan wuyan marigayin , sai kuma kusa da aka buga masa a ka, sannan ga sara a wuyarsa ta bangare biyu, sai kuma aka daura filo a kansa wanda ya jike “sharkab” da jini.
dan uwan marigayin ya ce sun sanar da babban ofishin ’yan sanda na garin Keffi abun da ya faru a ranar, inda jami’an tsaro daga ofishin su ka taho gidan su ka dauki hoton gawar da kuma dakin, kafin daga bisani a ka binneta.
Wata majiya a sakatariyar Ma’aikatar (FCTA), inda marigayin ke aiki, ta bayyana cewa gabanin hutun Sallah, marigayin ya bukaci sauyin wajen aiki a sakamakon rashin jituwa da a ka ce yana  samu da wasu abokan aikinsa.
Wakilinmu ya tuntubi babban jami’in ’yan sanda na rundunar ’Yan sanda da ke jihar Nasarawa, inda ya tabbatar da faruwan al’amarin.