✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka gudanar da karamar Sallar lafiya a garin Jos

Dubban al’ummar musulman garin Jos babban birnin Jihar Filato sun gudanar da karamar sallar bana lafiya, ba tare da samun wata matsala ba, a jiya…

Dubban al’ummar musulman garin Jos babban birnin Jihar Filato sun gudanar da karamar sallar bana lafiya, ba tare da samun wata matsala ba, a jiya Talata.

Tun da farko rundunar ‘yan sandan Jihar Filato ta tanadar da jami’ai guda dubu 2,181 da za su bayar da tsaro a lokacin bukukuwan sallar, tare da haramta amfani da kekunan NAPEP a lokacin bukukuwan sallar, don ganin an gudanar da bukukuwan lafiya.

Tun da farkon sanyin safiyar ranar ta Talata ne wakilinmu ya ganewa idonsa, yadda dubban al’ummar musulman na garin Jos suka yi ta tururuwa zuwa manyan masallatan idin garin na Ali Kazaure, da kuma na hanyar Bauchi Road da ke garin na Jos.

Da yake gabatar da huduba ga dubban al’ummar musulman da suka halarci masallacin Idi na Ali Kazaure. Babban Limamin Jos Sheikh Lawal Adam ya yi kira ga al’ummar musulmi su cigaba da yin koyi da abubuwan da suka koya, lokacin Azumin watan Ramadan.

Ya yi kira ga matasa su guji aikata miyagun abubuwa kamar sara suka da shan miyagun kwayoyi.

Har’ila yau ya yi kira ga al’ummar Najeriya su zauna lafiya domin sai da zaman lafiya ne za a iya samun komai na ci gaba.

Daga nan ya yi addu’ar Allah ya taimaki shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin jihohin kasar nan, wajen jagorancin al’ummar kasar nan bisa nasara.

Shima da yake gabatar da nasiha ga dubban al’ummar musulmin da suka halarci masallacin Idi na hanyar Bauchi Road shugaban majalisar malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’iqamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta tsayar da tashin farashin kudin zuwa aikin hajji daga Najeriya.