✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka kai wa masu rawa hari a Saudiyya

Jami’an tsaro a Saudiyya sun kama wani mutum da ya daba wa wadansu ’yan rawa guda uku wuka. An bayyana cewa mutanen sun samu rauni…

Jami’an tsaro a Saudiyya sun kama wani mutum da ya daba wa wadansu ’yan rawa guda uku wuka.

An bayyana cewa mutanen sun samu rauni a harin wanda ya faru a dandalin casu da ake gudanarwa a Riyadh don nishadi, a wani sabon al’amari ga wadansu ’yan kasar wadanda a baya suke ganin haramtacce ne.

Wani bidiyo da ke yawo a kafofin sadarwa na Intanet ya nuna yadda ’yan rawar ke cashewa, sanye da tufafi masu kyalkyalin zinari, sai kwatsam ba zato ba tsammani, wani mutum ya zaro wuka da tsawonta ya kai santimita 30 ya afka wa tawagar da ke casun a kan dandali.

Daga bisani mutumin ya zame ya fadi, sai kuma jami’an tsaro suka shiga tsakani.

Maza biyu da mace daya ne maharin ya yanka da wuka, amma an ce ba su ji rauni sosai ba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya ya bayyana maharin a matsayin dan shekara 33 dan asalin kasar Yemen kamar yadda BBC ya ruwaito. amma ba a bayyana manufarsa ba ko dalilin da ya sa ya kai harin ba.

Ana gudanar da casun ne a Dandalin Sarki Abdallah, kuma bikin ya kasance daya daga cikin casun da ake gudanarwa na tsawon wata biyu.

Hukumomin Saudiyya sun ce suna son samar da kudin shiga Dala biliyan 64 daga bangaren nishadi daga cikin matakan rage dogaro da man fetur.

Shekarun baya dai wani ba zai taba mafarkin za a gudanar da irin wannan casu ba a Saudiyya, amma Yarima Mohammad bin Salman ya kawo sababbin sauye-sauye da suka hada da bude gidajen sinima tare da kashe kudade wajen hada casu ga manyan mawaka irin su Janet Jackson da shirya damben zamani na maza da mata da kuma bai wa mata izinin tukin mota.

Sababbin sauye-sauyen sun fusata wadansu malaman kasar, sai dai suna samun karbuwa daga matasan Saudiyya.