Da Dumi Dumi

‘Yadda aka sace mana yara aka sayar kuma aka sauya rayuwarsu’

A makon jiya ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta kubutar da yara tara, wadanda aka sace su aka kuma sayar da su a Jihar Anambara.

Kwamishinan ’yan sandana Jihar Kano, Ahmed Iliyasu ya ce da yawa daga cikn yaran an sace su ne tun a shekarar 2014, inda Kwamishinan ya ce wani mutum ne mai suna Sagir ne ya sanar da su batun bacewar yara masu yawa a unguwarsu.

A cewarsa asirin masu satar yaran ya tonu ne a lokacin da shugabansu, Mista Paul Onwe da matarsa Mercy suke kan hanyarsu ta gudu da daya daga cikin yaran da suka sace zuwa garin Anacha.

Kwamishinan ya ce sun sace yaron mai suna Haruna Sagir Bako a lokacin da yake dawowa daga Makarantar Islamiyya da misalin karfe 6:00 na yamma a ranar 11 ga Satumban bana. Ya ce lokaci da ake yi wa wadanda ake zargin tambayoyi, sun amsa laifinsu inda suka jagoranci jami’an tsaro suka gano yara takwas da aka riga aka sayar a Anambra.

Kwamishinan ya ce, wadanda ake zargin sun hada baki ne suka sace yara a unguwannin da suka hada da Sauna da Kwanar Jaba da Kawo da Hotoro da ’Yankaba da Dakata dukkansu a birnin Kano.

ADVERTISEMENT

Daga cikin wadanda aka kama da ake zargi da sace yaran akwai Paul Onwe da matarsa Mercy Paul da Ebere Ogbodo da Loiusa Duru da Monica Oracha.

Yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, wanda ake zargi da jagorantar sace yaran, Paul Onwe ya ce ya samu kimanin Naira miliyan biyu a wannan harka. Ya ce a cikin shekara biyar ya sace yara bakwai, ya tafi da su Anambra, inda yake samun Naira dubu 200 kan kowane yaro.

Mista Paul, wanda dan Jihar Ebonyi ne  da ke zaune a Kano tun 1990, ya ce wani Mista Emmanuel Igwe ne ya sanya shi a ciki harkar. “Wannan mutumin ne ya sanya ni a harkar, inda ya gaya min cewa Madam Ebere wacce ke sayar da abinci ce take neman yaro saboda ba ta da ko daya. Don haka ta sanar da matata, ita kuma ta shiga lalube. Yaron da na fara sacewa daga cikin bakwai, na sace shi ne a Unguwar Kwanar Jaba kuma an biya ni Naira dubu 150 a kansa,” inji shi.

Madam Ebere ta ce, Emma ne ya hada ta da Paul wanda ya gaya mata cewa matarsa tana aiki a gidan marayu.  Ta ce ta sayi yaran ne don ta rike su, saboda ba ta da da ko daya. “Ni ban taba haihuwa ba, lokacin da na gaya wa Emma matsalata, cewa maigidana ya kore ni a kan rashin haihuwa. Daga nan ya hada ni da Mista Paul, inda ya kawo mini yara biyu, wadanda na saya a kan Naira dubu 200. Daga nan na sanya su a makaranta.”

Na sha ganin Madam Ebere tana sayen yaran a gabana – Faruk

Yayin da yake tattaunwa da Aminiya, yaron da ta saya mai suna Faruk, wanda aka canja masa suna zuwa Onyedikabo Ogbodo, wanda aka sace shi yana dan shekara 5, ya ce tun daga lokacin da aka kai shi wurin uwar dakinsa Madam Ebere a Anacha, bai manta da gidansu ba; domin a cewarsa lokaci zuwa lokaci shi da sauran yara irinsa sukan tattauna yadda aka dauko su daga garinsu, aka kai su garin na Anacha. “Ni da wata yarinya mai suna A’isha, wacce aka sauya mata suna zuwa Ojoma, mukan zauna mu yi hira yadda aka rabo mu da iyayenmu; aka kawo mu garin Anacha,” inji shi.

Yayin da yake tuno yadda ya bar gidansu zuwa Anacha, Faruk wanda a yanzu haka yake tare da iyayensa, ya ce: “Lokacin da Paul ya kai ni Anacha akwai wani mutum da ake kira Emma. Na ga wannan mutum (ya nuna wani yaron daga cikin wadanda aka kubutar) suna tare suna wasa. Emma ya sayo min Cheese balls (cizi) kafin Anti Ebere ta zo ta dauke ni daga bisani ta kai ni asibiti; inda aka yi mini kaciya.”

Da yake bayanin abubuwan da yake yi a kullum, Faruk ya ce “Idan na tashi da safe zan wanke bakina sannan in yi wanka. Daga nan sai in shirya zuwa makaranta. Idan aka dawo sai mu je shago, inda Madam Ebere take sayar da abinci. Idan yamma ta yi sai in je in wanke kayan makaranta sannan in sake dawowa shago. Za mu zauna a shago har dare sannan mu dawo gida. A ranakun karshen mako kuma muna zuwa debo ruwa da safe idan mun tashi, gidan ba ruwa a famfo. Haka kuma a ranar Lahadi muna zuwa coci.”

Fauk ya ce yana aji hudu na firamare a Anacha kafin a kai ga kubutar da shi. “A lokacin zamana a Anacha, na yi makarantu har guda uku, Confidence Nursery and Primary School, sannan aka canja min zuwa Debine. A wannan makarantar na kai aji hudu na firamare.”

Ya ce uwar rikonsa ba ta azabtar da shi, sai dai idan ya yi abin da ba daidia ba “Ba ta azabtar da ni haka kuma ba ta hana ni abinci, domin abinci birjik yake a gidanta, kasancewar harkar abinci ne sana’arta. Idan ka ga ta dake ni, to na yi laifi, misali idan ban wanke kayan makarantata ba,” inji shi.

Faruk wanda ya ce a zamansa na shekara biyar ya ga yadda ake cinikayyar yaran Hausawa da ake kawowa zuwa Anacha. “Ni ne farkon yaron da aka fara kaiwa gidan Madam Ebere, ban dade ba sai ga shi an kawo wadansu tagwaye mata daga Kano wato Husna da Amira. Daga baya sai na fahimci ita ma tana sayar da yaran da ake kawo mata daga Kano ga wadansu mutane daban a cikin garin Anacha. Ba zan iya kirga lokacin da na ga Madam Ebere tana kirga kudi tana ba wa Emmanuel ba. A gabana aka sayar da Amira domin har an dauke ta zuwa wani wuri daban, kafin ’yan sanda su zo su kubutar da mu,” inji shi.

Faruk ba ya son yin Sallah – Mahaifinsa

Malam Ibrahim Ahmad Salisu shi ne mahaifin Faruk, ya shaida wa Aminiya cewa a yanzu haka yana fuskantar kalubale da yaron, kan yadda ba ya son yin Sallah da kuma kin cin abincinsu. “Yanzu babban kalubalen shi ne, ya dawo ba ya son yin Sallah haka kuma ba ya son cin ire-iren abincinmu. Idan ban da shinkafa ba ya cin komai. To a haka dai ake maleji a sama masa dan abincin da ya saba ci, kin dai san yanayin abincin Kudu ba daya ne da namu ba,” inji shi.

Mahaifiyar Faruk ta ce batan da ya yi tsawon shekara biyar ya haifar mata da cutar jiri. “Ko a zaune nake sai in ji kaina yana juyawa sai dai in kwanta. Amma yanzu alhamdu lillahi muna cikin farin cikin da ba zai misaltu ba amma dai ciwo ya riga ya shiga jikina, domin ko bayan da aka gan shi yanzu sai da ciwon ya tashi,” inji ta.

Wacce ta sace mu ta gaya mana za ta ba mu alawa – Husna da Amira

Husna da Amira suna daga cikin yaran da aka kubutar daga hannun barayin mutanen  a garin Anacha. Duk da cewa ba tagwayen asali ba ne, domin iyayensu ne ’yan uwa, wadanda kuma gidajensu ke makwabtaka da juna. Hakan ne ya janyo shakuwar yaran har wadansu ke zaton tagwaye ne, sun kasa tuno zamansu na makonni a garin Anacha, sai dai suna tuno zaman da suka yi a gidan Paul, bayan da matarsa ta sace su daga unguwarsu.

“Lokacin da matar ta dauke mu a kofar gidanmu, ta ce mu biyo ta za ta ba mu alawa. Sai Husna ta bi ta, ni sai na ki na juya da gudu, sai na fadi sai matar ta zo ta daga ni sannan ta goya ni. Ta kuma rike hannun Husna. Daga nan muka tafi gidanta,” inji ta.

’Ya’yana ba su yi gaggawar tahowa wurina ba da farko – Auwalu

Malam Auwalu Murtala wanda aka fi sani da Auwalu Ango, shi ne mahaifin Amira da Husna, ya ce sun shiga dimuwa lokacin da aka sace ’ya’yansa a ranar 5 ga Satumban bana. “Tun daga lokacin da aka sace yaran muka shiga dimuwa da tashin hankali. Amma gaskiya mun yi addu’a sosai har Allah Ya kawo mu inda Ya sake hada mu a yau,” ini shi.

Ya ce a yanzu haka suna cikin farin cikin bayyanar ’ya’yansu, inda ya jinjina wa ’yan sanda bisa kokarin da suka yi wajen kubutar da yaran.

Gwamnati za ta kafa kwamiti mai karfi – Ganduje

Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdulahi Umar Ganduje ya yi alkawarin ganin cewa gwamnati ta tabbatar da an yi adalci a kan yaran da aka sace aka sayar da su a Anambra. A wata takarda da Mai taimaka wa Gwamna kan Hulda da Jama’a, Malam Abba Anwar ya sanya wa hannu, Ganduje ya ce za a gurfanar da mutanen da suka hada baki wajen sayar da yaran a kotu don ganin sun fuskanci hukunci daidia da laifinsu.

“Satar yara babban laifi ne, musamman   kananan yara. Abu ne da gwamnati da duk wani mai hankali yake Allah-wadai da shi. Don haka ba za mu zuba ido mu ga wadanda ake zargi su sha ba,” inji Gwamnan

A cewar Ganduje, gwamnati za ta hada kai da jami’an tsaro tare da kafa kakkarfan kwamiti don tabbatar da an binciko tare da zartar da hukunci a kan duk wanda ke da hannu a wannan lamari. “Muna shirin kafa kwamiti mai karfi da zai binciki ainihin lamarin don magance abin a nan gaba. Haka muna kira ga iyaye su kara kula da duk wani motsi na ’ya’yansu don ganin sun tsira daga fadawa hannun miyagu,” inji shi.

Barista Abdu Bulama Bukarti lauya ne mai fafutikar kare hakkin dan Adam, ya ce lauyoyi da dama a jihar sun kafa wata kungiya mai suna ‘Justice for 47’ don ganin an hukunta wadanda ake zargi da sacewa da sayar da wadannan yara kamar yadda doka ta tanada..

“Wanann kungiya ce mai neman tabbatar da adalci a kan yara 47 da aka sace a Jihar, Kano wadanda zuwa yanzu aka samu wadansu daga ciki. Don haka za mu bi hakkin yaran nan wajen ganin an yi wadanda ake zargi da laifin sace su hukunci mai tsanani, lura da irin laifin da suka aikata,” inji shi.

Tuni kungiyoyin Musulmi da na shiyya da kuma daidaikun mutane da suka hada da Jama’atu Nasril Islam da Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah da Fityanul Islam da Kungiyar Kare Hakkin Musulmi (MURIC) da ta dattawan Kano ta KCCI da Kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) da Sanata Shehu Sani duk sun yi Allah wadai da sace yaran inda suka bukaci a gudanar da gagarumin bincike don gano sauran yaran da aka sace tare da hukunta masu hannu a lamarin.

Fitaccen dan jaridar nan mai gidan rediyon Human Right da ke Abuja, Ahmad Isah da aka fi sani da Ordinary President ya bayar da gagarumar gudunamwa wajen bankado wadanda suka saci yaran bayan daga farko jami’an tsaro sun ki daukar mataki kan korafin da iyayen yaran suka kai musu game da wadanda suka sace yaran nasu.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya