✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi addu’ar ukun Sarkin Zazzau

Dubban jama'a sun halarci addu'ar ukun rasuwar Sarkin Zazzau Shehu Idris

An gudanarar da addu’o’in cika kwana uku da rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris a fadarsa da ke birnin Zariya.

Dubban jama’a ne suka taru domin addu’ar ciki har da tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo da Gwamna Nasiru El-Rufai da takwaransa na Jihar Jigawa, Muhammadu Badaru.

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero na daga cikin mahalartar addu’ar da ta gudana a safiyar Laraba.

A ranar Lahadi 20 ga Satumba, 2020 ne Allah Ya yi wa Sarki Shehu Idris rasuwa bayan shafe shekara 45 a kan karagar mulkin Masarautar Zazzau a matsayin sarki na 18 .

Ya bar duniya yana da shekara 84 da haihuwa bayan fama da rashin lafiya.

Daga hannun dama Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti; tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo (a tsakiya) da Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai (da shudin kaya).
Daga hannun dama Obasanjo ne da Kayode Fayemi sanye da fararen kaya, sai tsohon Gwamnan Kaduna, Mukhatar Ramalan Yero da tsohom Mataimakin Shugaban Kasa Muhammad Namadi Sambo da sauran mahalarta.
Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo yana jawabi a taron addu’ar ukun Sarkin Zazzau, Shehu Idris.
Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar zuwa wurin addu’ar ukun.
Wani sashe na mahalarta addu’ar ukun a Fadar Sarkin Zazzau da ke Zariya.
Obasanjo da El-Rufai da sauran mutane sun daga hannu a lokacin da ake gudanar da adduar
Wani sashe na sarakai da manyan mutanen da sauka halarci adduar