Search
Subscribe
Yadda aka yi hawan Sallah a Legas da wasu jihohin Kurmi

Yadda aka yi hawan Sallah a Legas da wasu jihohin Kurmi

A Jihar Legas da ma sauran jihohin Kudu Maso Yamma, an yi bikin Sallah karama lafiya cikin walwala, inda a mafi yawancin masallatan yankin aka yi Sallar Idi da misalin karfe 10 na safe. A wasu masallatan sun yi da misalin karfe 9:45, wasu kuma karfe 9:50 kana a bana mafi rinjaye na al’ummar Musulmin wannan yanki sun yi Sallar Idi a ranar Talatar da ta gabata kamar yadda aka yi asassan kasar nan da dama, kana ba a sami matsalar ruwan sama ba, da a lokuta da dama kan kawo cikas a irin wadannan lokuta na Idi a wannan yankin.

A masallacin garin Agege Limamin garin Sheikh Sharif Habib Abdull-Majid, ne ya bada Sallah idin a karkashin jagorancin Sarkin Agege Alhaji Musa Dogonkadai inda a hudubar sa ya yi kira ga al’umma da tasirantu da kyawawan dabi’un da suka koyar a lokutan Azumin Ramadan yayin da a kasuwar Mil12 a Legas Limamin da ya yi Sallah ya yi huduba akan munin zagin shugabanni. Haka zalika Mai martaba Sarkin Hausawan Agege Alhaji Mujammadu Musa Dogonkadai ya yi kira ga al’umma da su zamo masu son zaman lafiya da yi wa shugabanni da’a.

A jihar Osun a yankin Ifon an yi Sallar Idi, ne inda aka yi huduba aka kuma fassara ta da harshen Hausa da na Yarbanci lamarin da ba kasafai aka cika samu ba a masallatan Kudu maso Yamma, inda mafi yawanci ake samun masallatan Hausawa daban na Yarbawa daban sai dai a garin Ifon na jihar Osun Musulman garin wadanda suka hadar da baki ’yan Arewa masu sana’ar goro da ’yan kasa Yarbawan yankin suna yin Sallar idi a waje guda ne, inda ake yin wa’azi da huduba a harsunan Hausa da Yarbanci, Limamin da ya jah sallar idin Shaikh Abubakar Iliyasu limamin Ifon, ya shaida wa Aminiya cewa, al’adar garin ce haka duba da hadin kai da ke tsakanin su, ya ce ya yi hudubar sa ne a kan tsoron Allah tare da yi masa biyayya sau da kafa ako wane lokaci, haka zalika sarkin Hausawan garin Ifon Alhaji Mujammadu Sulaiman Sabo, ya mika sakon Sallar sa inda ya jaddada kalaman zaman lafiya, ya kuma shaida wa Aminiya cewa, kowa ka gani a garin Ifon yana da sana’a wannan shi ne dalilin zaman lafiyar su, ”Mu a nan zaune muke lafiya da Yarbawan wannan yanki akwai dangantakar alakar auratayya da kasuwanci a tsakanin mu, ko ni da kake gani na auri mata Bayerabiya yanzu haka tana gida na don haka duk mun zama abu guda“. In ji shi.

Bikin Sallar karama ya yi armashi sossai a jihar Legas dama sassan jihohin Kudu maso Yamma, inda jama’a suka fito cikin ado na kawa maza da mata, yara da manya aka yi ta hada-hada duk da kokawan da wasu ke yi na rashin kudi hakan bai hana jama’a yin hada-hadar Sallah ba, domin kuwa anyi hidindimun Sallar ko wane mutum ya yi daidai gwargwadon ikon sa, sannan abu mafi mahimmanci a yi bikin Sallar cikin salama da walwala.

 

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin