✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi ruwan ‘alburusai’ a birnin Rum na Italiya

A ranar Asabar da ta gabata ce wani jirgin sama kirar Boeing 787 ya samu matsala jim kadan bayan ya tashi, inda nan take gisalan…

A ranar Asabar da ta gabata ce wani jirgin sama kirar Boeing 787 ya samu matsala jim kadan bayan ya tashi, inda nan take gisalan jirgin suka fara fashewa suna zubowa kasa a birnin Rum na Italiya.

Nan take mutanen birnin na Rome musamman wadanda suke kusa da filin jirgin Rum suka hargitse suka shiga rudani, inda har wadansunsu suka fara buya saboda gilasan na zuba kamar alburusai daga sama.

Yanzu haka ana bincike a kan yadda jirgin ya samu matsala, wanda hakan ya ji wa akalla mutum daya rauni. Sannan gilasai masu nauyi kamar duwatsu suka bata motoci da gidaje da sauransu.

Wani ganau ya shaid awa wata jaridar Italiya mai suna II Messaggero cewa, “Gilasan sun zubo ne kamar alburusai. Shi ya sa muka fara gudu muna buya.”

Wani ganau shi ma ya ce, “Abin ya yi kama da tsawa mai karfi, amma lokacin ana rana ne mai zafi, kuma ko hadari babu. Sai na fita daga rumfar da nake ciki, inda na ga ashe ruwan karafa ne da gilasai nan take na fara gudu ina ihu har na samu na buya.”

A cewar wata majiya, akalla motoci 25 da gidaje 12 suka lalace, sannan wani dattijo mai shekara 54 ya ji rauni sosai, wanda har aka kwatanta shi da cewa, “ya yi sa’ar tsira da ransa.”

Daga baya sai wadansu daga cikin mutanen garin suka fito cikin rudani da mamaki, inda suka rika tsintar gilasan jirgin wanda girmansu ya kai santimita 10 zuwa 20.

Magajin Garin Rum, Esterino Montino ya tabbatar da aukuwar lamarin a shafinsa na Facebook inda ya bukaci a yi gaggawar daukan mataki domin kare sake aukuwar lamarin. “Da misalin karfe 4 da minti 40 na yamma a ranar Asabar, wani jirgin sama da ya tashi daga filin Jirgin Leornardo da Binci ya samu matsala jim kadan bayan tashinsa, wanda ya sa dole ya dawo. Amma a lokacin da yake kokarin sauka, wasu gilasai da karafa sun zubo da karfi a garin Bia Marriotti a yankin Isola Sacra. A lokacin da suke zuba, sun barnata motocin mutane da ke ajiye da rufin gidaje da sauransu, wanda hakan ya sa ’yan sandan yankin Carabinieri da ’yan kwana-kwana da takwarorinsu suka kai dauki yankin.

“Wannan lamarin ya kara tabbatar da maganar da muke yi tuntuni cewa akwai matsalar tsaron lafiyar mutane a wannan yanki. A gwamnatance mun sha yin magana game da yadda wajen tashin jirgin ya yi kusa da mutane. Saboda haka ne muka shiga yarjejeniya da Hukumar ADR domin kada jirgi ya tashi da dare har sai gari ya waye sosai, amma yarjejeniyar ba ta yi amfani ba.

Kakakin Kamfanin Jirgin Saman, wanda na kasar Norway ne ya shaida wa Euronews cewa jirgin wanda ya tashi daga Rum da nufin zuwa Los Angeles a Amurka ya samu matsala jim kadan bayan tashi, amma cikin sauri direban jirgin ya yi saukar gaggawa a filin Jirgin Fiumicino, “amma jirgin ya sauka lafiya.”