✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake ci gaba da zawarcin ’yan wasa

  Bayan rufe kasuwar saye da sayar da ’yan wasan kwallon kafa a watan Janairu, kungiyoyi suna ci gaba da hange da neman ’yan wasa…

 

Bayan rufe kasuwar saye da sayar da ’yan wasan kwallon kafa a watan Janairu, kungiyoyi suna ci gaba da hange da neman ’yan wasa domin cike gurbin da suke bukata a watan Yuni da asalin kasuwancin ’yan wasan ke kankama. A watan Janairu ana cin kasuwar ce ta takaitaccen lokaci, amma ana cin kasuwar ce sosai a watan Yuni, kamar yadda BBC ya tattaro.

Manchester United na fatar shiga gaban Chelsea inda za ta ware Fam miliyan 120 wajen sayo dan wasan gaba na Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho, mai shekara 19.

Ita ma Liberpool na shirin sabunta kwangilar dan wasan bayanta na Netherlands Birgil ban Dijk, mai shekara 28, inda za a rika biyansa sama da Fam 150,000 a mako.

Haka Manchester United na iya sabunta bukatarta kan dan wasan Lyon mai shekara 23 Moussa Dembele.

Tottenham za ta ware Fam miliyan 40 domin karbo dan wasan Bournemouth Nathan Ake, mai shekara 24.

Chelsea na sa ido kan dan wasan Moroko Hakim Ziyech bayan ta kasa karbo dan wasan mai shekara 26 daga Ajad a watan Janairu.

Ajad na tunanin sayo dan wasan baya na Tottenham da Belgium, Jan Bertonghen, inda kwangilar dan wasan mai shekara 32 za ta kawo karshe a karshen wannan kakar.

An gano kocin Tottenham Jose Mourinho yana kallon wasan da Bayern Munich ta yi kunnen doki da RB Leipzig ranar Lahadi, inda ake tunanin saboda dan wasan baya na Leipzig na Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 21.

Babban abin jan hankali kan rade-radin kasuwancin shi ne Jubentus na zawarcin kocin Manchester City Pep Guardiola kuma za su bari dan kasar Spain din mai shekara 49 ya fada musu duk bukatun da yake so a biya masa.