Search
Subscribe
Yadda ake dahuwar ‘Creamy garlic chicken’

Yadda ake dahuwar ‘Creamy garlic chicken’

Assalamu alaikum uwargida. Yaya sanyi? Tare da fatar ana cikin koshin lafiya. Har ila yau dai a ci gaba da bada shawara a kan gwada girka abincin Turawa koda sau daya ne a mako ga maigida don canza salon girki a gida da kuma kwarewa a wajen dafa su a yau na kawo muku wani salon girkin Turawa da za a iya cin miyar da dafaffiyar taliya ko farar shinkafa. A ci dadi lafiya.

Abubuwan da ake bukata

• Kaza

• Garin albasa (za a iya samu a manyan shagunan da ake sayar da kayan girki).

• Garin masoro

• Dakakken barkono

• Garin tafarnuwa

• Magi

• Man gyada

• Filawa

Hadi

Bayan an wanke kaji sai a yayyanka su sannan a zuba a cikin kwano sai a zuba garin tafarnuwa da masoro da garin dakakken barkono da magi sannan a kwaba su wuri daya sai a rufe a sanya a gidan sanyi na tsawon awa daya.

Bayan haka, sai a dora tukunya a wuta sannan a zuba man gyada bayan ya yi zafi sai a zuba kazar mai hadin a ciki a rika juya ta har sai ta nuna sannan a tsame a ajiye a gefe.

Man da aka soya kazar da ya rage sai a zuba kwabin fulawa a ciki a yi ta juyawa na tsawon minti biyu. A jajjaga tafarnuwa sannan a zuba a hadin fulawar da ruwan madara sannan a zuba su magi da garin masoron da kuma kazar a ciki sai a mayar kan wuta ana juyawa har sai miyar ta yi kauri sannan a sauke.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin